Jarumin Film Din Hausa, Adamu Zango Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

Dan wasan kwaikwayo na Hausa, Adamu Zango ya fice daga jam’iyar A, P, C. Jarumin wasan hausa Zango ya bayyana cewa ya fita ne daga cikin tafiyar ne sakamakon rashin mutuncin da ake masa a cikin jami’iyyar ta A, P, C.
Ya kara da cewa ya kashe sama da Miliyan biyu wajen yawan kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari dama A, P, C gaba daya amma babu abinda jam’iyyar ta bashi a matsayin sa na wanda yake bada gudunmawa a tafiyar ta buhari.
Adamu yace, harkar siyasa ba Addini bace dan haka yana da dama yayi wanda yake ra’ayi a matsayin sa na dan wasan kwaikwayo na hausa. Wanda ya shahara a idon duniya dan haka ya bayyana ficewar daga A, P, C zuwa jam’iyyar P, D, P, ya koma bayan Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Da yake bayani Zango ya yi kira zuwa ga duk masoyan sa a duk fadin Nigeriya cewa duk su zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasa a wannan zabe da za a yi ranar 16 ga watan nan.
Ya fadi abinda ya fata masa rai a cikin tafiyar A, P, C inda yace “Buhari bai san shiba, Gwamnan Kaduna Nasiru El’ Rufa’i bai san shi. Gwamna Masari bai san shi ba a matsayin sa na wanda yake yi musu kamfen domin su lashe zabe.
Sannan kuma ba a taba yaba mini ba ko kuma a bani kudi ba, hakan ta sanya na chanza ra’ayina na koma jam’iyyar wadanda suka san mutuncina suka san amfani na.
Sai de kuma mutane da dama suna tofa albarkacin bakin su na ficewar tasa. Inda suka ce kwadayin kudi ne kawai ya sanya sa chanza ra’ayi. Amma Zango ya musanta zargin.

Exit mobile version