CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Jawabin Shugaban Kasar Sin Na Murnar Shiga Sabuwar Shekara Ta 2021

by CRI Hausa
December 31, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
5 min read
Jawabin Shugaban Kasar Sin
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A jajibirin sabuwar shekara ta 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi domin taya jama’ar kasar Sin da sauran al’ummar duniya murnar sabuwar shekara, ta babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG) gami da kafar yanar gizo ta Internet. Ga Jawabin nasa:

Aminai da abokai, maza da mata, barkanku da war haka. Yayin da shekarar 2021 ke karatowa, ina muku fatan alheri daga nan birnin Beijing

samndaads

A shekarar 2020,shekara ce ta musamman a gare mu. A lokacin da aka samu barkewar annobar cutar COVID-19 ba zato ba tsammani, mun tsaya kan manufarmu na mai da jama’a da rayukansu a gaban kome, inda jama’armu suka nuna kishin kasa, da jajircewa, da kokarin hadin kai, inda suka kafa tarihi bisa kokarinsu wajen ganin bayan wannan annoba. Lokacin da muke haye wahalhalu tare, inda muka samu jaruman da suka shiga cikin wuraren da ake samun bullar annoba don kai gudummawa a wurin, da mutanen da suka tsaya a wurin aikinsu ba tare da saduda ba, da wadanda suka yi kokarin tinkarar annoba tare, da wasu da suka nuna cikakkiyar jaruntaka yayin da suke sadaukar da rayukansu, gami da mutanen da suka yi kokarin zaman “cude ni in cude ka”. Daga likitoci zuwa sojoji, da masu nazarin kimiyya da wadanda suka samar da hidimomi a ungwanni, da masu aikin sa kai, da ma’aikatan gine-gine, da tsofaffi, da matasa, wadanda dukkansu suka shiga ayyuka na kubutar da jama’a, ba tare da fargaba ba, inda suka hada karfi da karfe don samar da cikakkiyar kariya ga rayukan jama’a. Yadda suka nuna sadaukarwa, da kokarin hadin gwiwa da juna don samar da taimako, da abubuwan da suka sosa ran jama’a, ya nuna wani ruhun da muke samu a zamaninmu na kokarin dakile annoba. ‘Yan kananan ayyukan da aka yi a rayuwar yau da kullum sun samar da babbar gudunmowa, kana ana samun jarumai ne a cikin jama’ar kasarmu. Kowanenmu ya yi wani babban aiki mai muhimmanci! Ina so in nuna jajantawa ga wadanda suka kamu da cutar COVID-19! Da jinjina ga dukkan jaruman da suke zama tare da mu! Ina alfahari da kasarmu da jama’armu, da wani ruhu na al’ummarmu na kokarin daidaita yanayin da ake ciki ba tare da kasala ba.

Ana nuna jaruntaka tare da samun kwarewa a aiki ne idan aka shiga mawuyacin hali. Bayan da muka yi nasarar dakile annobar COVID-19, mun kuma raya tattalin arziki da zaman al’umma. Yanzu haka, mun kammala dukkan ayyukan da muka tsara a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13, kana mun yi nasarar tsara dukkan fannonin ayyukan da za mu gudanar bisa shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14. Muna kokarin kafa wani sabon tsari na neman ci gaban kasa, da aiwatar da shirin raya kasa tare da tabbatar da bunkasuwa mai inganci. Daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, kasarmu ce ta fara samun farfadowar tattalin arziki, kana ana kyautata zaton cewa ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasarmu cikin shekarar 2020 zai kai matsayin kudin Sin RMB triliyan dari. A fannin samar da hatsi, muna samun girbi mai armashi a shekaru 17 a jere. Aikinmu na nazarin kimiyya da fasaha shi ma ya samu ci gaba sosai, ta la’akari da yadda muka samu nasarar harba na’urorin bincike na “Tianwen-1”, da “Chang’E-5”, da “Fen Dou Zhe”, da dai sauransu. Kana muna kokarin gudanar da aikin gina tashar ciniki cikin ‘yanci a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Ban da wannan kuma, mun tinkari matsalar mummunar ambaliyar ruwa, inda sojoji da fararen hula suka hada kai wajen tinkarar bala’in, inda suka samu babbar nasara. Yayin da na kai rangadi a wasu larduna, da yankuna, da kuma birane 13, na ga yadda dukkan jama’a suka yi kokarin aiwatar da matakan kandagarkin annoba a tsanake, da neman farfado da ayyukan samar da kayayyaki, da yunkurin kirkiro sabbin fasahohi. Mutane a ko ina a kasarmu suna cike da imani, da jajircewa, tare da kokarin raya kasarsu.

A bana, mun shirya wasu manyan bukukuwa don murnar cika shekaru 40 da kafa yankin musamman na raya tattalin arziki na Shenzhen da sauransu, da cikar shekaru 30 da fara raya yankin Pudong na birnin Shanghai, da aiwatar da manufar bude kofa a yankin. A birnin Shenzhen dake bakin tekun kudancin Sin, da birnin Shanghai dake bakin kogin Huang-pu, ana iya ganin abubuwa masu burgewa sosai. Inda wasu manufofin na gwaji yanzu haka sun zama abin koyi ga sauran wurare, kirkire-kirkiren da aka gudanar a baya yanzu sun zama jagora wajen aiwatar da sabbin manufofinmu. Babbar manufarmu ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje ta sa mun samu wani abin al’ajabi a fannin ci gaban tattalin arziki. Nan gaba za mu kara kokarin zurfafa gyare-gyare, da kara bude kofarmu, don samar da karin ci gaba ga ayyukanmu na fannoni daban daban.

Mai adalci ba shi da matsalar kadaici, kuma mu al’ummar duniya ‘yan uwan juna ne. Wahalar da muka sha a shekarar da ta gabata, ta sa mun kara fahimtar muhimmancin al’ummar duniya mai makoma ta bai daya, idan an kwatanta da sauran lokutan baya. Na tattauna da wasu sabbi da tsoffin abokai na kasashe daban daban, tare da halartar taruka ta kafar bidiyo, inda batun da aka fi magana a kai, shi ne hadin gwiwa da juna don dakile cutar COVID-19. Har yanzu akwai jan aiki. Ya kamata jama’a na kasashe daban daban mu hada karfi, don ganin bayan cutar COVID-19 nan da nan, da kuma gina duniyarmu da kowa zai ji dadin zama.

Shekarar 2021, shekaru 100 ke nan da kafa jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A cikin shekaru 100 da suka wuce, jam’iyyar ta gudanar da wasu manyan ayyuka, kuma har yanzu ba ta manta da manufar kafa ta ba. Tun da aka kaddamar da jam’iyyar a ginin Shi-Ku-Men dake birnin Shanghai, da gudanar da taronta na farko a cikin wani kwale-kwale a tabkin Nanhu dake garin Jiaxin, ya zuwa yanzu jam’iyyar dake rike da ragamar mulkin kasar Sin ta girma sosai, sabo da kokarin da ta yi wajen biyan bukatun jama’a, baya ga wahalhalu da yawa da ta haye. Jami’iyyarmu za ta ci gaba da dora cikakken muhimmanci kan jama’a, da tunawa da nauyin da jama’a suka dora mata, da kokarin aiki don neman cimma burin raya al’ummar kasar Sin.

Yayin da muke kokarin aiwatar da shirinmu na raya kasa na “Shekaru dari daya” guda biyu, za mu fara aikin mu na gina wata kasa mai bin tsarin siyasa na gurguzu ta zamani. Duk da cewa ayyuka suna da yawa, amma wajibinmu ne mu gudanar da su. Ta hanyar kokarin aiki, mun daidaita matsaloli, tare da samun ci gaba. Nan gaba za mu kara mai da hankali a kan aiki, don tabbatar da wata makoma mai haske.

A wannan lokaci, an fara kunna fitilu, kana iyalai suna taruwa. Sabuwar shekara tana nan tafe, abin da muke fatan gani shi ne samun kwanciyar hankali da ci gaba a kasarmu. Da fatan kowa da kowa zai kasance cikin koshin lafiya da zaman alheri.

Na gode sosai!

SendShareTweetShare
Previous Post

Sin Ta Amince Da Nau’in Farko Na Rigakafin COVID-19 Da Aka Samar A Cikin Kasar

Next Post

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar 2021 Ga Masu Sauraro Da Masu Kallo

RelatedPosts

Wane Irin Tsarin Cudanyar Tattalin Arzikin Duniya Ake Bukata?

Wane Irin Tsarin Cudanyar Tattalin Arzikin Duniya Ake Bukata?

by CRI Hausa
12 hours ago
0

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, wasu mutane sun...

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

by CRI Hausa
12 hours ago
0

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya saurari...

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

Jiangxi: An Taimakawa Mutane Wajen Saukaka Begen Gida Da Suke Yi Ta Kafar Bidiyo Kai Tsaye

by CRI Hausa
12 hours ago
0

A kauyen Huikeng a garin Xinwan na gundumar Xiushui a...

Next Post
Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar 2021 Ga Masu Sauraro Da Masu Kallo

Jawabin Shugaban CMG Na Murnar Sabuwar Shekarar 2021 Ga Masu Sauraro Da Masu Kallo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version