Tare da Kabir Sa’idu Bahaushe
kibdau:kabeerlokuacious77@gmail.com
Babu tantama Ko shakka Matasa a kodayaushe abin alfarin kasa ne da al’umma,wadanda idan ba mu yi alfahari da su ba to mun yi gwari. Domin su ne za su dauko hanyar gina rayuwar al’umma da kansu,abin da yake a gaban masu ruwa da tsaki kawai mu tuntuda su a matattakalar nasarar rayuwa da abin da muke iyawa. Alhaji Sani Sabulu Na-Kanoma ya ce:
Wai Yaro ka daura kaya,
Bai tashi dauka ba.
A cikin watan da aka yo ranar Matasa ta Duniya a 12 ga watan Agustan, 2017.Inda matasan kasar nan sama da milyan 70 kididdiga ta nuna ba su da ayyukan yi, wanda haka dole ne a nemi hanyar daure wannan kalubalen da ke a gabansu da je-ka-hudar koyar da sana’o’i, domin hakan ne kadai zai iya fidda a’i ga rogo.
A irin lokacin da daliban da suka gama jami’a a kasarmu, kashi daya cikin dari ne suke samun aikin gwamnati, inda kashi 10 cikin 100 kuma ke samun ayyukan yi a kamfanoni masu zaman kansu.Ke nan har yanzu da karatu kadai babu sana’a ba a sha ba, wai an danne bodari ta ka.
Idan wani kamfani matashi ke yi wa aiki,samun sa zai takaita ne matuka na abin da ake biyansa kadai. Amma da zarar matashi na sana’a to samunsa zai kasance yana karuwa sosai gare shi ko kuma wasu na yi masa aiki.
A irin cibiyoyi koyar da sana’o’in da ke akwai na gwamnati da masu zaman kansu na kyauta da na kudi ana kyankyasa mai kyau, ta yadda matasa za su zama masu dogaro da kansu da kuma ba da ayyuka ga jama’a, dama su ne kashin bayan kowace al’umma.
Ba kowace makarantar boko ba ce ba take iya koyar da sana’a, ko kuma ake samun horo na sana’a. Neman ilimin ake yi a kuma samu ya cigaba da amfani, ya kuma amfanar ya zama Nagge dadi goma.
Wani fitacce ta fuskar ci gana ya taba cewa “Ba zan taba bari makaranta ta shiga cikin ilimina ba”.
Wannan hanyar ta koyin sana’o’i mai bullewa ce ko ba a yi ratse ba, sannan kuma linzamin zama mai dogora da kai ce, kamar kuma yadda take da ginannen gida na rufin asirin rayuwa da taimakawa al’umma da kuma kishinta.
Don haka dukkan Matasa masu baiwa ne da basirar zama abin da muke so mu zama; kada mu yanke basirarmu ta hanyar awon kwalwar da muke yi wa kanmu na gazawa da kasawa.
Matsayinka na matashi kada ka kuskura ka yaudari kanka da ilimin takarda kadai, don shi ba dalili ba ne ko hujjar karshe ta gwada fasaha da kuma kwarewarka.
Mutane suna koyo ne ta hanyoyi da mabambanta masu yalwa, don haka kada ka takaita basirarka a tunani daya kawai sai ka fara ginin fadada shi tun daga yanzun nan.
Don haka kada wanda ya kara jiran aiki ga gwamnati, kawai ka kirkiri ayyuka da yawa sosai.
Ga wasu ‘yan misalai, wanda ya fara zuwa duniyar wata Werner Bon Braun ya fadi lissafi har karo uku, amma kuma mai ganewa ne sosai.
Don haka sana’a ba a ja mata lokaci, da ka samu dama ka fara kawai.Tsayawar da kake yi, kana ragewa kanka ne samun nasara.
Zai kuma taimake ka matuka ka tafi da zamani domin gudun yin cumbu ko sabkon bubukuwa.
Ina masu sha’awar koyon dinki? Akwai wani matashi da ya kammala jami’a ba shi da ko sisi, saboda yana samun kudi ne ta hanyar kudaden makarantar da ake ba shi a gida. Watarana sai wani abokinsa ya ziyarce shi, sai ya ga rigar abokin ta burge shi matuka, ya bukace shi da ya sai da masa ita. Yana sai da masa, sai dubara ta fado masa cewa ashe ma ana sai da kayayyaki, don haka daga nan ya zama fitaccen telan zamani da ya samu nasara.
Za ka iya gamuwa da kalubalen rashin nasara a sana’arka ko rashin jari, kada ka damu da wannan domin duk fitattu yawanci a duniya ba daga gidan masu kudi suke ba. Irin su Oprah Winfrey, Bill Gates, Stebe Jobs wanda ya sai da motarsa, abokinsa kuma ya sai da Babbar na’urar lissafinsa suka kirkiri kamfanin Apple wanda yanzu haka shi ne babba a duniya. Da Jack Ma da sauransu.Ke nan kana iya sai da wata kadara ka yi jari da ita ba sai ka jira tallafi ba kullum kamar yadda muke dakushe kanmu a yanzu.
- Babu dalilin da matashi zai zama ba mai sana’a ba.
- Duk wanda ya ce maka ba ka iyawa,ba aboki ba ne ba, abokin kirki zai yi imanin cewa za ka iya kawai.
- Matashi ya tabbata ya duk mafarkinsa ya zama gaskiya. Domin duk abubuwan da ka gani na amfani a Duniya su jirgi, wayar salula, motoci duk mutane ne da ba su fi ka hikima ba suka yi su, idan dai har za su iya to kai ma za ka iya.
Mu hadu mako mai zuwa…