Sani A. Anwar" />

Jerin Manyan Kusoshi A Nijeriya Da Suka Kamu Da Cutar Kwarona

Tun bayan da aka samu wasu a Nijeriya da ke dauke da Cutar Kwarrona (Cobid-19) inda daga ranar 27 ga watan Fabrairun wannan shekara, a kullu yaumin ana kara samun yawaitar masu kamuwa da cutar.

A ranar 7 ga watan Afrilu da misalign karfe 09:30 na dare, an samu tabbacin mutane 254 wadanda ke dauke da wannan cuta ta Cobid-19 a Nijeriya daga Cibiyar kula tare da hana yaduwar cutuka ta kasa (NCDC). Inda aka kuma bayar da tabbacin mutuwar mutane 7 tare da sallamar kimanin 44 bayan sun warke daga wannan cuta.

Kazalika, mafi yawancin wadanda aka samu da wannan cuta, mutane wadanda a kusa-kusan nan ke da tarihin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ko kuma yin mu’amala da su. A cikin wadannan manyan mutane ko masu rike da madafun iko a Nijeriya akwai wadanda suka warke bayan sun jima suna fama da ita, a karshe kuma aka tabbatar da cewa ba sa dauke da wannan cuta Cobid-19.

Ga dai jerin wadannan manyan kusoshi a Nijeriya wadanda suka kamu da wannan cuta, lokaci bayan lokaci bayan yi musu gwaji aka kuma same su da ita.

  1. Abba Kyari

A ranar 24 ga watan Mayun wannan shekara ne aka sanar da cewa, Babban Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Tarayya, ya kamu da wannan cuta ta Cobid-19. Bisa dukkanin alamu kuma, ya kamu da cutar ne a yayin da ya yi tafiya Kasar Germany da kuma Egypt. Inda daga bisani a ranar 29 ga watan Mayu, aka garzaya da shi zuwa Jihar Legas domin yi masa magani.

  1. Nasir El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, shi da kansa ya bayyana a shafinsa na twitter cewa, an yi masa gwaji, an kuma tabbatar da cewa yana dauke da wannan cuta ta Cobid-19. Sannan, a halin yanzu yana nan yana samun kulawa ta hanyar shan magani.

  1. Bala Mohammed

Shi ma Gwamnan Jihar Bauchi, an bayar da sanarwar yana dauke da wannan cuta a ranar 24 ga watan Mayu, bayan an yi masa gwaji. Kamar yadda rahotannin suka bayyana, Gwamnan ya dawo Jihar Bauchi daga Legas, inda ya hadu da dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar a jirgi, wanda shi ma aka same shi dauke da wannan cuta. Kamar yadda dai rahoton ya bayyana, sun yi musabiha da juna tare da tattaunawa a tsakaninsu a cikin wannan jirgi da suka hau tare, inda ake kyautata zaton a wannan haduwa ne Gwamnan ya kamu da wannan cuta.

  1. Seyi Makinde (ya warke)

Haka nan, Gwamnan Oyo, a ranar 30 ga watan Mayu aka tabbatar da tasa kamuwar daga wannan cuta. Kamar yadda aka bayyana a halin yanzu cewa, ya warke bayan sake yi masa wani gwajin a karo na biyu, amma duk da haka yana nan a kadaice.

  1. Mohammed Atiku Abubakar

Kamar yadda aka sani, Mohammed guda ne cikin ‘ya’yan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar. Mahaifin nasa ne a ranar 22 ga watan Mayu, ya sanar da cewa, dan nasa na dauke da wannan cuta. Tun bayan wannan lokaci kuma, yana can a Abuja yana karbar magani yana kuma samun sauki kamar yadda ya bayyana da kansa.

 

  1. Chioma Rowland

Sannan Chioma, budurwar Mawakin nan mai suna Dabid Adeleke, wanda aka fi sani da Dabido, ita ma ta kamu da wannan cuta ta Cobid-19. Dabid din ne ya bayyana haka, a shafinsa na Instagram cewa budurwar tasa na dauke da wannan cuta, sannan shi da sauran mutanensa su 31 za su je a yi musu gwaji sakamakon tafiya da suka yi zuwa Kasar Amurka.

  1. Farfesa Jesse Otegbayo (ya warke)

Shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kwalejin (UCH) Ibadan, Farfesa Jesse Otegbayo, shi ma an tabbatar day a kamu da wannan cuta ta hanyar yin gwaji a ranar 29 ga watan Mayu. Wanda shi ma tuni aka bayyana cewa, ya warke ta hanyar sake yi masa gwaji a karo na biyu.

  1. Muhammed Babandede

Muhammed Babandede, Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa, kamar yadda ya bayyana da kansa, ya killace kansa tun bayan dawowarsa daga Kasar Ingila a ranar 22 ga watan Mayun wannan shekara, inda ya zargi kansa da kamuwa da wannan cuta.

  1. Farfesa Ezekiel Olapade-Olaopa

Shugaban Jami’a na Kwalejin Lafiya, Farfesa Ezekiel, shi ma ya kamu da wannan cuta ta Cobid-19, bayan yi masa gwaji. Kamar yadda rahotanni suka nuna kuma, a halin yanzu babu wasu alamu da ke nuna cewa yana dauke da wannan cuta, duk da cewa yana cigaba da karbar magani.

  1. Farfesa Obafunke Denloye

Farfesa Obafunke, Shugaban Kwalejin Lafiya na Jami’ar Ibadan, shi ma na cikin guda daga cikin manyan kusoshin wannan kasa, wadanda suka kamu da wannan cuta ta Koronabairus a Nijeriya.

 

Exit mobile version