Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Kamu Da Korona A Gasar Turai

Korona

An fara gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 ranar 11 ga watan Yuni a birane 11 da ke fadin nahiyar sai  dai kuma cutar korona ta ci gaba da kama wasu ‘yan wasan da ke killace kansu, wasu ma har hakura suka yi da gasar.

Tuni dai wasannin na bana suka yi nisa, domin an kai fafatawar zagaye na biyu, har an fitar da mai rike da kofin Portugal da Faransa da Croatia da Wales da Austria da kuma kasar  Netherlands.

Tun a shekarar 2020 aka tsara gudanar da gasar cin kofin nahiyar Turai, amma bullar cutar korona ta sa aka dage wasannin zuwa bana kuma nan gaba shekara uku kacal za ayi kafin a sake gudanar da wasa gasar.

‘Yan wasan da suka kamu da cutar korana a Euro 2020:

Croatia

Iban Perisic ya kamu da cutar korona ranar 26 ga watan Yuni kuma Croatia ta fafata da Sifaniya ba tare da Iban Perisic ba a wasan zagaye na biyu, bayan da dan kwallon mai shekara 32 ya kamu da annobar.

Ingila

Ben Chilwell ya killace kansa ranar 21 ga watan Yuni sannan Mason Mount – ya killace kansa ranar 21 ga watan Yuni sannan Ben Chilwell da kuma Mason Mount sun killace kansu har sai ranar 28 za su fito, ba su buga wa Ingila karawa da Jamhuriyar Czech ba, bayan da suka yi cudanya da dan wasan Scotland, Billy Gilmour, wanda ya kamu da cutar korona.

Netherlands

Mai tsaron raga Jasper Cillessen ya kamu da cutar korona ranar 28 ga watan Mayu kuma mai   tsaron ragar tawagar Netherlands ya hakura da gasar ta bana, bayan da ya kamu da annobar, kuma mai koyarwa, Frank de Boer bai yi niyyar jiran sai ya warke ba.

Portugal

Shima Joao Cancelo  ya kamu da cutar korona ranar 12 ga watan Yuni kuma mai tsaron bayan tawagar ta Portugal bai samu shiga wasannin bana ba, bayan da ya kamu da annobar, inda Diogo Dalot ya maye gurbinsa, bai samu buga wasan da tawagar ta yi da Hungary ba.

Rasha

Dan wasa Andrei Mostoboy shima ya kamu da cutar korona ranar 11 ga watan Yuni sai dai kasar Rasha ta maye gurbin Andrei Mostoboy da mai tsaron baya Roman Yebgenyeb, sakamakon da Mostoboy ya kamu da annobar.

Slobakia

Denis Babro ya kamu da cutar korona ranar 17 ga watan Yuni

Kuma mai tsaron baya Denis Babro da wani mamba a tawagar sun kamu da annobar a karawar da za suyi da Sweden amma mai koyawar Stefan Tarkobic ya ce dukkansu suna cikin koshin lafiya, ba alamar kamuwa da annobar a jikinsu.

Sifaniya

Dan wasan Barcelona Sergio Buskuets  ya kamu da cutar korona ranar 6 ga watan Yuni sai dai  kyaftin Sergio Buskuets ya kamu da annobar kwana takwas kan wasan farko da Sifaniya za ta kara da Sweden, saboda haka bai buga karawar ba shi kuwa mai tsaron baya, Diego Llorente ya kamu da cutar kwana biyar kan Sifaniya ta yi karawar farko ta cikin rukuni da Sweden.

Sweden

Dejan Kulusebski  ya kamu da cutar korona ranar 8 ga watan Yuni sannan Mattias Sbanberg – ya kamu da cutar korona ranar 8 ga watan Yuni amma dan wasa Dejan Kulusebski da kuma Mattias Sbanberg ba su buga wa Sweden wasan farko na cikin rukuni da Sifaniya ba, sakamakon kamuwa da cutar korona.

Bayan da tawagar ta buga wasan farko ne ‘yan wasan biyu suka koma yi mata wasa, bayan da aka sake gwada su ba a samu cutar a jikinsu ba kuma yanzu sun murmure kamar yadda mai Magana da yawun tawagar kasar ya bayyana.

Exit mobile version