Jibi Asabar Za A Yaye Kuratan Sojoji Karo Na 80 A Dafot Ta Zariya

Daga Isa Abdullahi Gidan Bakko,

Yanzu haka rundunar sojojin Nijeriya wato Depot Nigerian Army Chindit Cantoinment da ke Zariya ta kammala duk shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da bikin yaye sabbin kuratan sojoji karo na tamanin.

Bayanin haka ya na kunshe ne a cikin wata takarda wadda mataimakin jami’in da ke hulda da jama’a na rundunar, Kaftin Audu Arigu, wanda kuma rundunar ta raba wa manema labarai a Zariya shirye – shiryen bikin da aka ambata.

A cewar takardar, wannnan biki da zai gudana a ranar Asabar mai zuwa 29 ga watan Mayun wannan shekara gta 2021, zai gudana ne a filin faratin sojojin da ake kira RSM Hama Kim Parade Ground da karfe takwas na safiyar wannan rana da aka ambata.

Kamar hyadda takardar da Kftin Audu ya sa wa hannu, wannan bikin kammala horas da kuratan sojojin an tsara yin sa ne a ranar Asabar 22 ga watan Mayun da mu ke ciki, amma saboda matsalar hadarin jirgin saman day a faru, da ya yi sanadin rsuwar babban kwamnandan sojojin Nijeriya Laftana Janar Ibrahin Attahiru a ranar Juma’a 21 ga watan Mayun wannan shekara da mu ke ciki, wanda shi ne zai jagoranci bikin da za a yi.

Zuwa hada wannan labara, duk inda ka za ga a cikin harabar barikin sojojin na Depot da ke Zariya, babu abin da za ka gani sai shirye – shiryen gudanar da wannan taro na kammala horas da kuratan sojojin karo na 80, kamar yadda aka bayyana a baya.

Exit mobile version