Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

JIBWIS Ta Yi Tir Da Korar Fulani Daga Wasu Jihohin Yamma

by Muhammad
February 19, 2021
in LABARAI
2 min read
JIBWIS
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Lawal Umar Tilde,

Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Izalatil Bid’ah ‘Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS), na kasa Shiekh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ya yi Allah wadai da ganin yadda wadansu tsirarun mutane suke neman haddasa fitina a tsakanin al’ummar kasar nan. Shiekh Jingir, ya bayyana haka da lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Jos fadar gwamnatin Jihar Filato, bisa korar Fulani makiyaya da aka yi daga Jihoyin Oyo da Ondo, tare da kone shagunan al’ummar Arewacin kasar nan mazauna Jihar Oyo, a bisa wani sabani da ya shiga tsakanin wani mutumin Arewa da Bayerabe a jihar.

samndaads

Ya nuna bakin cikin ganin yadda wadansu mutane daga cikin al’ummar kasar nan da ke neman rura wutar fitina don kawai su sami cimma burin kansu ba tare da yin la’akari da idan wutar ta tashi har da su za ta cinye ba. Ya ce kasa kamar Nijeriya mai yawan mutane sama da miliyan 200 kuma mafi karfin tattalin arzikin kasa a nahiyar Afrika, ba wayewa ba ce wata kabila ta rika kyamatar wata kabila a kasar tun da kundin Tsarin Mulkin kasa ta bai wa kowannenensu ‘yancin zama duk inda yake so ya kuma gudanar da sana’arsa ba tare da wani ya tsangwame shi ba.
Shiekh Jingir, ya kuma yi gargadi da kakkausan harshe ga duk wata kabila da take ganin za ta samun nasara idan ta haddasa fitina a kasar nan, sai ya kara da cewa duk wani rikici na addini ko na kabilanci ba zai haifar wa kasar nan da mai idoba. A karshe ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su kara hada kansu, sannan su guji ta da duk wata fitina da za ta kawo cikas da barazana ga kyakkywan zaman lafiya a sakanin kibilun kasar nan, yana mai cewa al’ummar kasar nan basu da wata kasa a fadin duniyi da tafi Nijeriya idan ta salwanta kowa zai yi na dama.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kwastam Ta Cafke Kayan Sama Da Naira Miliyan 300 A Kebbi, In Ji Kalla  

Next Post

An Daina Fashin Zuwa Aiki A Karamar Hukumar Kunchi – Shuwaki

RelatedPosts

Hadiza Usman

Hadiza Bala Usman Ta Yi Ta’aziya Ga Iyalan Marigayi Dikko Inde

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga Abdullahi Sheme A ranar juma'ar da ta gabatane shugabar...

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

Masana Sun Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Sake Nada Hadiza Bala Usman Shugabar NPA

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Daga Bello Hamza, Abuja Masana da masu ruwa da tsaki...

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

An Sako Daliban Da Aka Sace A Zamfara

by Muhammad
6 hours ago
0

Rahotanni daga jihar Zamfara sun tabbatar da cewa an ceto...

Next Post
Kunchi

An Daina Fashin Zuwa Aiki A Karamar Hukumar Kunchi - Shuwaki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version