Kwamitin sulhu na musamman na Jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin tsohon Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ne suka kai masa wannan ziyarar.
A shekarar da ta gabata ne jam’iyyar PDP ta kafa kwamiti na musamman domin sulhu a tsakanin ‘yayanta. Saraki ne ya sanar da wannan ganawar ta shafinsa na Tuwita, @bukolasaraki.
“A yunkurinmu na sauraron manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyarmu, a yanzu haka kwamitin sulhun PDP na ganawa da tsohon Shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ,” inji Saraki.