Muhammad Maitela" />

Jihar Borno: Gobara Ta Lashe Gidajen ’Yan Gudun Hijira 1,200

Akalla gidajen ’yan gudun hijira guda 1,200 ne wata mummunar gobara ta lakume a makon da ya gabata a sansanin ’yan gudun hijirar da ke zaune a kauyen Gajiram a karamar Hukumar Nganzai da ke Jihar Borno, a wata sanarwar da gwamnati ta fitar jiya.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa, gobarar ta faru ne tun ranar 24 ga Oktoba, al’amarin da ya jawo kimanin ’yan gudun hijira 7,200 su ka rasa matsuguninsu.
Har wala yau, sanarwar ta kara da cewa, wannan gobarar, “ta na daga cikin munanan tashin gobarar da matsugunin ’yan gudun hijirar Gajiram ke fuskanta kusan kowace shekara.”
A yayin da ta ke tabbatar da afkuwar gobarar, shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA), Hajiya Yabawa Kolo, ta ce, gobarar ta kone sansanin bakidaya. Ta kara shaida da cewa, wannan ibtila’i ne wanda ke faruwa kusan a kowace shekara, “kuma hakan ya na da alaka da tsarin rayuwar jama’ar garin,” in ji ta.
Ta cigaba da cewa, “mafi yawan mutanen kauyen su na yin al’adanci girke-girkensu a waje kusa da dakunansu a lokacin hunturu, yayin da iska ta na kadawa da karfi, wanda cikin kankanin lokaci sai ka ga dakunan jama’a sun kama da wuta, wanda nan take su ke konewa kurmus.”
Hajja Kolo ta kara da cewa, hukumar SEMA ta gudanar da bincike a cikin jama’ar da lamarin ya shafa tare da bai wa ’yan gudun hijirar daukin gaggawa.
“Binciken da mu ka gudanar ya nuna jimillar magidanta 1,200 ne gobarar ta shafa,” in ji ta.
“SEMA ta samu umarni daga Gwamnan Jihar Borno wajen bai wa jama’ar tallafin gaggawa, wanda a ranar Lahadi mun bai wa kowane mutum daya buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25, wake da masara ga wannan adadi na magidanta 1,200 tare da gidan sauro da barguna.
“Bugu da kari kuma, mun samu tallafin Naira miliyan uku daga Sanata mai wakiltar Arewacin Jihar Borno a Majalisar Dattijai da taimakon Naira miliyan daya da rabi daga dan Majalisar Wakilai, Hon. Muhammed Monguno, mai wakiltar Monguno, Nganzai da Guzamala,” ta bakin Hajiya Kolo.

Exit mobile version