Sani Hamisu" />

Jihar Borno Na Bukatar Malamai 6,000 Domin Inganta Bangaren Ilimi – NUT

Kebbi

Jihar Borno na bukatar malamai sama da 6,000 domin inganta bangaren ilimi a fadin jihar bakidaya.
Wannan kira ya fito ne daga bakin kungiyar malamai ta jihar Borno, wato NUT, inda suka bukaci a inganta bangaren ilimi a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa kungiyar malaman ta yi watsi da sauye-sauye na karantun mega 40 da makarantu suka gina don magance ilimin yara 53,000 da kungiyar Boko Haram ta zaba su da matsugunin su.
Shugaban kungiyar na NUT, reshen jihar Borno, Jibril Muhammed, shine ya shaida haka ga NAN a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno,cewa akalla malamai sama da 5000 ake bukata a makarantun firamare yayin da za a kara 1000 zuwa ga sashin sakandare don bunkasa koyarwa da ilimantarwa a fadin jihar.
Ya yaba da gwamnatin jihar ganin yadda take kokarin sake farfado da sashin ilimi a jihar, amma yace ya kamata a fifita harkar ilimi fiye da komai saboda ta hanyar hakan ne ake samun ci gaban.
“Gwamnati na gina makarantun fasaha wanda dalibai za suyi karatu a ciki amma kuma sai de babu malamai.Ina da tabbatacin cewa idan aka fifita bangaren koyarwar malamai to za aga chanji mai dorewa a bangaren karatu.”
Daga karshe ya maimaita cewa malaman makaranta sun kasance cikin mummunan hare-haren Boko Haram, wanda akalla kimanin malamai 530 kungiyar ta Boko Haram ta kashe da 32,000 wadanda suka yi hijira.

Exit mobile version