Jihar Jigawa Ta Fara Raba Tallafin Cutar Korona Ga Nakasassu 1, 500

Daga Bello Hamza

A haliin yanzu gwmanatin jihar Jigawa ta fara raba katan 7,000 na kayan abinci ga masu fama da nakasa fiye 1,500 a fadin jihar, wannan na daga cikin kayan tallafin cutar korna da aka ware wa jihar.

Shugaban hadaddiyar kungiyar masu fama da nakasa a jihar, Malam Muhammad Usman, ya bayyana haka a tattauwarsa da manema labarai a garin Dutse ranar Asabar.

Bayani ya nuna cewa, kayayyakin da aka raba sun hada da tirela 94 dauke da katan 49,941 na kayan abinci daban daban wanda hukumar yaki da cutar korona (CACOVID) ta ba jihar a mastayin tallafi.

Ya ce, an shirya raba kayan agajin ne ga mutane masu fama da nakasa a fadin kananan hukumomin jihar 23.

Ya ce, kayan abinci sun hada da shinkafa da taliya ga garin masara da indomi da sauran su.

Shugaban ya kuma ce, za a raba kayan ne ga kurame da makafi da kutare da dukkan masu fama da nakasa a fadin jihar.

Ya kuma ce, wannan tallafin yana zuwa a kan lokaci ga masu fama da nakasa musamman ganin halin kunci da ake ciki a halin yanzu.

Ya kuma yaba wa gamayyar kungiyar CACOVID da gwamnatijn jihar a kan yadda ta yanke shawarar raba kayan tallafin ga masu fama da nakasa a jihar.

Daga nan ya kuma bukaci wadanda za su amfana da wannna tallafin su yi amfani da su yadda ya kamata.

Exit mobile version