Daga Bello Hamza,
Gwamnatin jihar Kaduna ta ware Naira Biliyan 4.6 don samar da kayan aiki tare da daga darajar asibitocin jihar a sabuwa shekara mai kamawa na 2021.
Wannan na daga cikin Naira Biliyan 9.1 da gwamnatin jihar ta ware wa ma’aikatar Lafiya a kasafin kudin shekarar 2021, kamar dai yadda manema labarai suka samu bayani a garin Kaduna ranar Asabar.
Bayanin kasafin kudin ya nuna cewa, an ware Naira Miliyan 2.0 don gina asibiti mai gado 300 da kuma Naira Miliyan 20.7 don sayen kayan aiki ga manyan asibitocin jihar.
Gwamnatin ta kuma ware Naira Milyan 22.5 gyara tare da sabunta bangaren kwantar da wadanda suka yi hatsari na manyan asibitocin jihar, Naira Miliyan 800 don samar da bangaren masu hatsurra na asibitin Doka.
An kuma ware Naira Miliyan 23.5 don samar da kayan lantarki a asibiti daya a kowannne mazabar majalisar dattawa na jihar da kuma Naira Miliyan 24.9 don sayen kayan tace jini ga masu cutar suga.