Jihar Katsina Za Ta Kashe Naira Bilyan 74 Kan Hanyoyi

Hukumomi

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Gwamnatin Jihar Katsina  bayyana cewar za ta kashe Naira biliyan 74 a kan aikin ginawa da kuma gyaran hanyoyi da suka kai kilomita 1,378 a fadin kananan hukumomin 34 na Jihar, domin magance matsalolin sufuri da mazauna karkara suke fuskanta.

Kwamishinan ayyuka da gidaje na Jihar, Mista Tasi’u Dandagoro, shi ne wanda ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan da gwamna Aminu Bello Masari ya duba ayyukan hanyoyin da ake gudanarwa a shiyyar  Daura, ya ce wannan gwamnati mai ci yanzu ta gaji ayyukan hanyoyi da yawa daga gwamnatocin da suka gabata.

A cewarsa, “Maganar gaskiya ce mun gaji ayyuka da yawa, daga cikin gwamnatocin da suka gabata in muka kammala ayyuka  13  muka kuma kashe jimillar  kudade sama da Naira biliyan 6.1 don kammala su wadancan  ayyukan.”

 

Kwamishinan ya bayyana cewar gwamnatin Jihar karkashin jagorancin Masari ta bayar da ayyukan hanyoyi 71 a fadin jihar, wadanda suka hada da hanyoyin  karkara 39, da suka kai fadin kilomita 461 wadanda za su ci sama da Naira biliyan 2.8 idan aka kammala su.

Ya  kara bayanin cewar “Yawan hanyoyin wannan gwamnati ke ke ginawa a karkashin jagorancin Gwamnanmu, Alhaji Aminu Bello Masari, idan aka kammala su, gwamnatin Jihar Katsina za ta kashe kimanin Naira biliyan 74 don ginawa da kuma gyara  hanyoyin da suka kai kilomita 1,378 a fadin jihar.

Daga cikinsu da akwai hanyoyin kauyuka guda 39 masu nisan kilomita 461 wadanda kuma ita gwamnatin Jihar Katsina za ta kashe jimillar kudi Naira biliyan 2 . 833 don aikin ginasu.

 

“Har ila yau kuma muna da ayyukan gyarawa na kimanin ayyuka 18 inda wannan gwamnatin za ta kashe sama da Naira biliyan 16 don ginin su. Kuma sauran kudin shi ne kudin da za a kashe kan sababbin ayyukan da wannan gwamnatin ta bayar da kwangilarsu. ”

 

Shi ma a nasa jawabin gwamna Masari ya ce gwamnatin Jihar ta ba da kwangilar gina hanyoyin Gurbin Baure-Shinfida-Batsari amma shi dan kwangilar bai kammala aikin ba,  saboda yadda shi al’amarin tsaro ya lalace sosai a wurin.

 

Ya ci gaba da bayanin cewa: “Mun kuma kammala binciken hanyar Kurfi-Birchi da Wurma, wannan kangilar ba za a samu aiwatar da ita ba, saboda yadda al’amarin ya tabarbare a wurin.  Hakanan ma hanyoyin Danmusa-Maidabino-Tsamiyar jino zuwa Kankara, mun kammala zanen yadda za a gina su hanyoyin, amma saboda rashin tsaro ba za mu iya ba da ita kwangilar ba.

 

“Bugu da kari kuma ita kwangilar yanzu ta hanyar Kankara-Dansabau wadda ta ke iyaka da Jihar Zamfara, dan kwangilar ya janye saboda rashin tsaro a yankin. Wadannan su ne manyan hanyoyin da matsalar rashin tsaro ta shafa. ”

Exit mobile version