Jihar Kebbi Ta Mika Yaron Da Aka Daure Da Sarka Bayan Shafe Wata 15 Ana Kula Da Lafiyarsa Ga Iyayensa

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi,

Gwamnatin Jihar Kebbi ta mika Jibril Aliyu, yaronsu dan shekara 11 wanda yanzu ya kai shekaru 12 da haihuwa a duniya da aka daure a turken dabbobi aka kuma barshi da yunwa tsawon shekaru biyu, ga iyayensa a unguwar Badariya a Birnin Kebbi.

Wakilin LEADERSHIP Hausa ya ruwaito cewa a ranar 9 ga watan Agusta, 2020, gwamnatin jihar ta yi alkawarin kula da lafiyar yaron, bayan da aka dauri da sarka da iyayensa suka yi masa.

Bayan xaure yaron da sarka, an gano cewa yana rayuwa ta dabba, kuma an tilasta masa cin abincin dabbobi, ba tare da shan ruwa ba, yayin da yake yawan cin najasarsa a matsayin hanyar tsira.

Da yake mika yaron ga iyayen, babban Daraktan kula da lafiya kuma babban sakataren din-din-din na asibitin tunawa da Sir Yahaya, Dakta Aminu Haliru Bunza, ya ce sama da kwararrun likitoci 20 ne suke duba lafiyar yaron yayin da yake zaune a asibitin na tsawon wata 15.

“A yau muna mika yaron da aka fi sani da Jibril ga iyayensa bayan ya zauna da mu tun daga ranar 10 ga watan Agusta, 2020 zuwa yau, kimanin watanni 15 kenan a asibitin tunawa da Sir Yahaya.

“Lokacin da aka shigo da shi yaron ya shiga cikin wani hali mai ban tausayi.

“A tsawon zamansa a nan, mu iya kula da lafiyarsa, mu kula da shi sosai, ta jiki da Kuma ta hankali.

“Yaron yana kwance a asibitin, kwararrun likitoci daban-daban sama da 20 na fannonin kiwon lafiya daban-daban da muke da su a nan, daga Asibitin Kolejin Jami’ar (UCH), Ibadan, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH) da sauransu domin a tabbatar da lafiyar sa.” Inji shi.

A cewarsa, yaron ya samu sauki sosai kuma gwamnatin jihar ta kula da shi xari bisa xari.

Dakta Aminu Haliru-Bunza ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da dorewar dangantakar da kuma taimaka wa yaron, inda ya ce akwai shirin ci gaba da kula da lafiyarsa da jin daxinsa.

“A wani ɓangaren na ci gaba da tallafin jinya, yaron kuma yana da inshorar hukumar kula da lafiya ta jihar Kebbi (KECHEMA), daga yau za a kula da shi har ya girma,” in ji CMD.

A nata jawabin, mai bai wa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu shawara kan harkokin mata da ci gaban al’umma, Hajiya Zara’u Wali, ta bayyana cewa, gwamnatin jihar ta samar da katafaren gida mai dakuna biyu ga yaron.

“Za mu tallafa masa da samar masa da bukatunsa da kuma alawus-alawus na wata-wata,” inji ta.

Ta kuma yaba wa Uwargidan Gwamnan, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, wadda ta bayyana a matsayin mai goyon baya da kuma jajircewa.

“Matar Gwamnan, ita ce kan gaba wajen tallafa wa yaron tun rana daya, kuma muna yaba mata tare da gode mata kan hakan,” inji ta.

Da yake mayar da martani, mahaifin yaron, Malam Aliyu Umar, ya gode wa Gwamna Bagudu da ya tallafa wa yaron da kuma yadda ya dawo da shi rayuwa bayan an yi masa magani da kuma gyara shi.

Sai dai mu ce, Allah Ya albarkace shi da iyalansa, Ya yi addu’a.

Exit mobile version