Connect with us

RIGAR 'YANCI

Jihar Kebbi Ta Rage Naira Biliyan 38 Daga Kasafin Naira Biliyan 138

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi ta rage Naira Biliyan 38 Kan Kasafin Kudin Jihar Kebbi na farko da da Gwamnan jihar ta Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya sanya wa Naira Biliyan 138 hannu tun farko.

Gyaran Kasafin Kudin Jihar ya biyo bayan matsalar da ke addabar al’ummar kasashen Duniya baki wato cutar Cobid 19 wanda ta yiwa tattalin arzikin kasa da jahohin illa . Bisa ga hakan ne gwamnatin jihar ta aikewa majalisar dokokin jihar don yiwa kasafin gyara domin gwamnatin jihar ta iya gudanar da ayyukkanta batare da wata matsala ba.
Kasafin na farko dai, Kasafi ne na Naira Biliyan 138 ne gwamnan ya sanya wa hannu kafin bullar cutar Cobid 19 .
Inda a cikin makon da ya gabata ne majalisar zartarwa ta jihar ta aikewa majalisar dokokin domin yin gyara ga Kasafin na farko da aka sanya wa hannu . Bisa ga hakan ne majalisar dokokin suka fantsama wurin tabbatar cewar sun yi gyara ga kasafin kudin na shekara ta 2020 daga Naira Biliyan 138 zuwa Naira Biliyan 99, 638 da ‘yan Kai. Wanda suka kammala gyran kasafin kudin cikin mako biyu kacal.
Haka kuma gyaran kasafin kudin ya shafi rage wasu manyan ayyukkan kamar gine-gine, shinfida hanyoyi da kuma rage yawan sayen motoci hawa na ma’aikata da kuma sauransu.
Saboda hakan ya zama wajibi ga manyan ma’aikatan gwamnatin da kuma sauransu su dauki hakuri har zuwa lokacin da tattalin arzikin kasa da na jahohin suka daidaita.
A jawabisa yayin da yake gabatar da sabon kasafin kudin da majalisar dokokin suka gyara, kakakin majalisar dokokin na jihar ta Kebbi, Samaila Abdulmumin Kamba ya ce” gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ta aikewa majalisar dokokin da bukatar gyaran kasafin kudin na jihar da aka sanya wa hunnu tun farko na Naira Biliyan 138 wanda a ranar 14 ga watan Yuli na shekara ta 2020 ne majalisar ta karbi don soma gyaran kasafin, inji shugaban majalisar dokokin “.
Ya ci gaba da cewar, “bukatar gyaran ta biyon bayan matsalar da aka samu kan bullar cutar Cobid 19 wanda ya janyo karewar tattalin arzikin kasa da na jahohin, haka kuma bayan majalisar dokokin ta karbi bukatar ta soma aikin gyaran kasafin kudin tun a ranar 14 ga watan Yuli inda mambobin majalisar suka kammala aikin gyaran a jiya wanda gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya sanya wa hunnu a jiya a Birnin-Kebbi, inji kakakin majalisar dokokin na jihar.”
An gudanar da bikin sanya hannu na kasafin kudin da majalisar dokokin suka gyara a dakin taro na fadar gwamnatin jihar ta Kebbi da Birnin-kebbi.
Shi ma a nashi jawabi yayin da ya sanya wa kasafin kudin da majalisar dokokin suka gyara hannu, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya “yabawa Mambobin majalisar dokokin kan irin namijin kokarin da suke yi na gyaran kasafin kudin a cikin mako biyu kacal , wanda ba karamin aiki suka gudanar ba, inji Gwamna Bagudu”. Ya kuma kara godewa sauran wasu manyan ma’aikatun da hukumomin gwamnatin jihar kan irin goyon bayan da suka bayar wurin ganin cewar an kammala gyaran kasafin kudin a cikin karamin lokaci.
Bugu da kari Gwamnan ya ce” wannan gyaran kasafin kudin bai shafi Albashi ba ko kuma mai kama da hakan ba . Ya ci gaba da cewar zai shifi manyan ayyukkan da gwamnatin jihar ke gudanar wa kamar gine-gine, shinfida hanyoyin mota da kuma rage yawan jinda di na manyan ma’aikata a jihar, inji Gwamna Bagudu “.
Daga karshe ya godewa dukkan Jama’ar da suka ba da tasu gudunmuwa wurin ganin cewar an gyara kasafin kudin jihar cikin lokaci.
Advertisement

labarai