Darekta karkashin ma’aikatar muhalli ta jihar Kwara Mista Towoju Gabriel, ya bayyana cewar jihar tana bukatar karin jami’ai, saboda a kula da tsaftace muhalli kamar yadda ya kamata.
Gabriel ya bayyana hakan ne lokacin daya gana da manema labarai a Ilori ranar Jumma’a ta wannan makon da muke ciki, cewar jihar tana bukatar jami’an kula da muhalli 2,000 ne, wanda a yanzu kuma 300 ne take dasu.
Ya ci gaba da bayanin cewar“ Muna bukatar jami’ai 2,000 ne a jihar amma kuma a halin yanzu 300 kawai muke dasu, da akwai bukatar a kara daukar irin wadannan jami’an kamar dai yadda ya jaddada ” .
Darekatan ya nuna damuwarsa yadda jihar take fama da karancin motocin zubar da shara, inda ya kara da cewar kadan daga cikin wadanda aka dasu sun tsufa, jkuma akwai bukatar a sauya su.
Amma duk da karancin motocin kwashe sharar da ake fuskanta ana kula da kawar da shara kamar yadda ya dace ta hanyar wayar da kan al’umma.
“Muna bukatar a cigaba da wayar da kan al’umma akai- akai ta kafofin watsa labarai kamar su Rediyo, Talabijin, da kuma sauran hanyoyin wayar da kan al’umma.
“A cikinm birnin Ilorin kowadanne ranakun Talata da Alhamis a n ba ‘yan kasauwa su share kasuwannin su tsakanin karfe bakwai zuwa tara na safe.
“Lahadin kowanne karshen wata an kafa doka wadda za a tsafatace muhalli n agama-gari, tsakanin karfe bakwai zuwa tara na safe wannan kowa da kowa ne zai kasance a cikin al’amarin tsaftace muhalli.
Ya yi kira da al’umma cewar su yi kokari su domin share su share muhallinsu na zama da kuma wuraren yin harkokin sun a yau da kullun.
Daga karshe Gabriel ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta samar da wuri a Sokoto-Ayekale akan hanyar Eyen-Korin inda za a rika zuba shara.