Jihar Kwara Za Ta Fara Daure Mashaya Giya Wata Shida A Gidan Yari

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja

Ga dukkan alamu Gwamnatin Jihar Kwara ta shirya bullo wa mashaya giya ta bayan gida, sakamakon sanya tarar Naira dubu dari ga duk wanda aka kama da laifin shan giya a bainar jama’a.

Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar ya rattaba hannu a kudirin dokar haramta sarrafa giyar, da sayar da ita da kuma kwankwadarta a wasu muhimman wurare na jihar.

Majalisar Dokokin Jihar ce ta yi kudirin dokar hukunta ‘yan giyar mai taken “dokar cikin birni ta shekarar 2018”. A karkashin dokar, an haramta wa duk wani mahaluki sayar da giyar ko adana ta ko kuma sha a bainar jama’a a wasu wuraren da ba a ambata ba.

Dokar ta yi tanadin cewa duk wanda aka kama da laifin karya dokar za a daure shi a gidan yari na tsawon wata shida ko biyan tarar Naira dubu dari (100,000) ko kuma hada wa mutum duka, ya biya tarar sannan a daure shi a gidan maza.

Matsalar shaye-shaye ta kasance a sahun gaba wajen rikitar da al’amura na zamantakewa da tattalin arzikin kasa a sassan Nijeriya. Inda hakan ya tilasta wa gwamnatoci fara neman dabarun shawo kan matsalar wanda matakin na Gwamnatin Kwara yana daya daga cikin na baya-bayan nan.

Shan giya wata muguwar jaraba ce wanda idan ta kama mutum tana da wahalar bari matukar ba a tashi tsaye ba. Galibin mashaya giya sukan ba da hujjar cewa idan sun sha tana sa su manta duk wata damuwa da ta addabe su. Sai dai malaman addini sun ce ko tana da amfani sharrinta ya fi yawa, inda suka kara da cewa giya ita ce uwar dukkan wani mugun aiki.

Exit mobile version