Connect with us

LABARAI

Jihar Nasarawa Ta Tallafa Wa Mata 300 Da Sana’o’in Dogaro Da Kai

Published

on

Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana cewa, za ta cigaba da shirin tallafa wa mata a jihar don karfafa harkokin tattalin arzikinsu da darajar.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyan haka a taron rufe horawar kwanaki biyar na koyawa mata sana’o’in dogaro da kai a jihar, an dai horar da mata 300 wadanda suka fito daga kananan hukumomi 13 na jihar sana’o’i daban daban.

Gwamna Sule, wanda mataimakinsa, Mista Emmanuel Akabe, ya wakilta , ya ce, an shirya hora da matan ne sana’o’i daban daban don rage tsananin talaucin dake addabar mata a jihar.

Ya ce, horarwa zai taimaka wa matan dogaro da kansu da kuma samun kudadan shiga, ta haka kuma darajar tattalin arzikinsu zai karfafa.

“Wannan shi ne babban daliln da gwamnatin jihar ta sanya makudan kudade duk kuwa da rashin kudade da ake fuskanta sakamakon annobar cutar korona a halin yanzu,” inji shi.

Gwamnan ya kuma taya wadanda suka kammala shirin horon murna ya kuma hore su dasu yi amfani da takardar shaidar da suka samu wajen bunkasa darajar rayuwarsu dana al’umma gaba daya.

A nata jawabin, kwamishiniyar mata da jin dadin al’umma, Hajiya Halima Jabiru, ta mika godiyarta ga gwamnatin ne akan yadda ta dauki lamurran mata a jihar da mahimanci.

Ta kuma kara da cewa, takardar shaidar da za a ba wadanda suka kammala shirin horrawar zai yi musu amfani wajen samun bashi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN).

A nata jawabin, daya daga cikin matan da suka amfana da shirin, Esther Awu, ta godewa Gwamnan jihar Abdullahi Sule da matarsa Hajiya Salifat Sule da kuma kamfanin da suka jagoranci horarwa, B – integrated Innobation Ltd., da wannan damar da suka samu na kara bunkasa harkokin rayuwarsu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: