Daga Sabo Ahmad.
Gwamnatin jihar Neja ta kara albashin ma’aikatan lafiya, tare da daukar ma’aikata dari hudu, don ta kai matakin albashin da gwamnatin tarayya ta kayyade.
Kwamishinan lafiya na jihar, Mustapha Jibril, ne ya bayyana haka ya yi da yake zanta wa da manema labarai a garin Makka da ke kasar Saudiyya. Mista Jibril, ya yi wanan maganar ce a madadin masu ruwa-da-tsaki a fannin lafiya na jihar. Ya kara da cewa, shekara biyu na mulkin gwamna Sani Bello, gwamnatin jihar ta kara yawan ayyukan da take yi wa jama’arta.
Sannan sai ya kara da cewa, “A fannin lafiya gwamnatin ta bunkasa kananan asibitoci, sannan kuma na gyara tare da daga darajar manyan asibitocin a wasu kanann hukumomi da ke jihar”
“A sheakara biyu da ta wuce, gwamnatin Sani Bello, ta gudanar da aikin fida da na idanu kyauta ga kusan mutum 4000 ‘ya asalin jihar Neja.”
A karshe, kwamishinan ya ce, diban ma’aikatan lafiyar, ya nuna yadda gwamna Sani Bello, ya damu da lafiyar al’ummarsa.