Jihar Neja Ta Yi Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda

Adamu Usman, wanda yake shi ne tsohon shugaban sashen kudi na hedikwatar rundunar ‘yan sanda dake Abuja, ya fara aikinsa a matsayin sabon Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Neja.  Usman ya canji Sabo Ibrahim wanda ya yi ritaya bayan ya shekara 35  yana aiki.

Wannan sanarwar ta fito ne a wata sanarwa da Kakakin hukumar ‘yan Sandar, Mohammed Abubakar,  na jihar ya fitar, inda ya ce Usman ya shiga aikin dan sanda ne a matsayin ASP a ranar 15 ga watan Maris din 1988, bayan ya kammala digirinsa na farko a bangaren sha’anin mulki a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a 1985.

Usman ya fara aiki a ranar Juma’a inda ya nemi hadin kan masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro a jihar, da kuma Sarakuna da shugabannin addini domin ganin an bankado masu aikata barna a jihar.

 

 

Exit mobile version