Jihar Neja Za Ta Daina Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa za ta daina hulda da ‘yan bindigar da suka addabi jiharta, sai dai kuma za ta yi amfani da sabon dabarar dakile ayyukan ‘yan bindigar a jihar.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Mary Berje, Sakatariyyar Yada labaran gwamnan, a sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis a garin Minna. Sakatariyyar ta nakalto Gwamna Abubakar Bello na fadin hakan ne a yayin ganawarsa da DIG AbdulMajid da Hosea Katma, AIG na shiyya ta 7 a gidan gwamnati dake Minna.

Gwamna Bello ya bayyana jin kunyarsa bisa yadda ‘yan bindigar ke ci gaba da kai hare-hare, inda ya ce yanzu lokaci ya yi da za su yaki ‘yan bindigar.

Ya yi kuma Allah wadai bisa hare-haren da ‘yan bindigar suka kai a kwanan nan suka kashe mutane a Galadiman Kogo dake karamar hukumar Shiroro, inda ya bayyana kai hare-haren a matsayin abin takaici kuma ba abin yarda bane.

Exit mobile version