Jihar Neja Za Ta Iya Ciyar Da Al’ummar Afrika — Nyaze

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Asabar din makon nan ne gwamnatin Neja ta dauki nauyin shirya taron tattaunawa ga mutanen Neja a kan canja fasalin kasa wanda ya gudana a babban dakin taro na mai shari’a Idris Legbo Kutigi da ke Minna.

Taron ya samu halarta kungiyoyi masu zaman kansu da ‘yan siyasa da ma wakilcin manyan mutane da ba su samu damar halarta ba.

Da yake bude taron shugaban jam’iyyar APC na Jihar Neja, Injiniya Muhammad Imam ya gabatar da wasu kudurce-kudurce wadanda suka kamata a tattauna a kansu kuma jama’a sun yi bayanai da daman gaske inda a karshe shugaban taron ya nuna farin cikinsa duk da rashin samun sakon jama’a a cikin lokaci, ya bayyana cewar al’ummar jihar nan daya ne daga cikin ginshikan cigaban kasar nan.

Daga cikin kudurce-kudurcen da aka gabatar sun hada da tsarin rabon arzikin kasa, da maganar kirkiro sabbin jahohi, da batun hanyoyin kudaden shiga na Gwamnatin Tarayya da jahohi har zuwa kananan hukumomi, yadda ake kashe kudade a majalisun tarayya da na jahohi, da batun rage karfi ga shugaban kasa, da tsarin tafiyar da mulki na karba-karba, da tafiyar da tattalin arzikin kasa da kuma gyara kan yadda ake gudanar da shari’o’i a kasar da yadda ake yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban ya ce, wadannan wasu muhimman bayanai ne da ya kamata al’ummar jihar su mayar da hankali dan bada nasu ra’ayin don ganin su ma sun samu damar tofa albarkacin bakinsu ga cigaban kasa.

Kwamishina a ma’aikatar sadarwa ta jihar, Mista Jonathan Tsado Batsa ya ce, maganar rashawa ai har yanzu ba a kama hanyar dakile matsalar ba, domin har yanzu siyasar ubangida na da tasiri, da ita kan ta gwamnatin ta samar wa jama’a madafa, da aikin maula ko roko bai yi tasiri wajen nada mukamai ba.

A cewarsa, “Kasar da ba ta da katamammen doka ga barawon gwamnati ko wanda aka kama da rashawa ai kuwa akwai sauran aiki, babban abin da ya wajaba gwamnati ta yi shi ne, ta mika kuduri a majalisar tarayya na samar da doka a kan duk wanda aka samu da rashawa ko satar kudin gwamnati, a samar da fursuna na musamman kuma a rika yanke masu hukuncin daurin rai-da-rai, ina da tabbacin za a iya samun nasara a kan wannan”.

Ya ci gaba da cewa, “Yanzu misali dubi kasar Sin, duk wanda aka samu da rashawa ko satar kudin gwamnati hukuncin kisa ake yanke masa, kuma dubi sauran kasashe irin su Rasha da makamantansu an wuce maganar rashawa ai, mu ma da za a iya dakile matsalar rashawa kawai da bangarori da dama an ci nasara a kansu”.

Sai kuma kuma maganar rabon arzikin kasa, inda ya ce muddin ba an dawo ana bai wa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba ne, ba ranar da za su iya tabuka abin da talaka zai yi na’am da shi. Tare da bda  misalign cewa, ya san irin kokarin da mai girma gwamnan jihar yake yi, amma yna tabbatar da idan za a wayi gari shugaban karamar hukuma bai iya gina ko da hanyar ruwa a karamar hukumarsa, lallai akwai gyara sosai. Kuma hakan bai samuwa sai an yaki rashawa da gaskiya, kuma mai yasa duk kokarin da hukumomin ke yi ba wani cigaba kuma bai hana abin da ake yi a cigaba da yinsa ba, rashin doka ne.

Dagan an sai ya yi nuni da cewa, babbar hanya mafi sauki a yanzu tun da a da wani tsari ingnatacce a kai, sai kowane dan kasa ya zama nagari, ya yi duba da kansa, wace hanya ce ya kama wadda ba za ta bulle ba to ya bar ta ya dawo kan ta kwaran.

A na shi wajabin, wanda ya wakilci mai girma gwamna kuma mashawarci na musamman a kan harkar siyasa, Mista Solomon Nyaze, cewa ya yi idan Gwamnatin Tarayya ta samar da yanayi mai kyau ko Jihar Neja na iya dogaro da kafarta. Ya ce jihar na daya daga cikin jihohin da Allah ya azurta da kasar noma saboda haka da suna da ingantaccen tsari ba Nijeriya ba ko Afrika jihar na iya ciyar da su da abinci.

“Yanzu ake cewa an fito daga matsin tattalin arzikin kasa, to ina matsin yake, ba wani matsi illa iyaka ba mu da ingantaccen tsari ne na dogaro da kai kullun an dogara da gwamnati, muna da kasar noma kuma muna da masu noman amma ba mai kulawa da abin da ake nomawa shi yasa noman ma sai ya zama kamar kawai kayan gado ne”, in ji Nyaze.

Nyaze ya ci gaba da cewa,  alal misali ka je kasar Bida, noman shinkafa sai ka rasa yadda za kai da kanka, ka zo kasar Minna, doya kuma sai ka rasa wajen zubawa, idan ka je kasar Kontagora masara da dawa kai har da wasu abubuwan da ake nomawa a wajen jihar ana iya nomawa. Amma abin tambayaa nan shi ne,  wane shiri gwamnati ta yi don cin moriyar wannan?”.

“A wajen rabon tattalin arziki ba jihar da ake tauyewa kamar Neja, domin mu a nan jihar ba mu morar arzikin da muke samar wa kasar ma, ana ba mu kashi talatin da takwas na abin da muke samarwa maimakon kashi hamsin din da ya kamata mu samu. Mu a nan ana tauye mu ne kuma majalisar kasa ta sani ba wani abin da aka yi don gyara, idan Neja-Delta na karbar kashi hamsin da doriya mu ke samar da wutan lantarki a kasar me yasa ake tauye mu, duk irin abubuwan da ya kamata a duba a gyara kenan amma ya gagara”, in ji Nyaze.

Muhammed Estu na kamfanin LEADERSHIP ya jawo hankalin taron ne gad a yadda sakacin gwamnati ya janyo masu mutuwar kananan sana’o’in hannu saboda rashin samar da wadataccen wutan lantarki duk da cewar jihar ce kan gaba wajen samar da lantarki a kasar nan.

Etsu ya cigaba da cewa, “Ana maganar samun kudaden shiga a jiha, ai mu ke da hanyoyin samun kudaden amma rashin inganta su shi yasa ita kanta gwamnati ke kokawa, Gwamnatin Tarayya da na jiha har da ita kanta karamar hukuma suna amsar haraji a hannun ‘yan kasuwa amma wani tanadi aka yi wa masu biyan harajin nan don cin moriyar abin da suke bayarwa, ya kamata gwamnati ta inganta muradunta, ta baje a faifai kowa ya san yadda ake kashe abin da yake bayarwa kuma ya ji abin a jikinsa”.

Manyan masana tattalin arziki da shari’a sun tattauna batutuwa da dama a kan wannan muhimmin taro, ciki har da wani mai sharhi a kan harkokin yau da kullum Hon. Dauda Yusuf Kontagora, wanda ya ce an bar ganga ne ana dukan taiki. A cewarsa, maganar gyaran fasalin kasa, su wane ne suka lalata ta, ai kasar tana da fasalinta illa iyaka son zuciya da rashin tsoron Allah na masu mulki.

Y ace duk irin dokar da za a kafa son zuciya ba zai bari tai aiki ba, duba da yadda Magu ke aiki yau, wa yake wa aikin, kuma tun da aka fara kashi dari na wadanda aka kama da rashawa mutum nawa aka daure? Babban matsalar za ka ji ana ta yekuwa a kafafen yada labarai amma bayan yekuwar me ake aiwatarwa? Da farko ma mu ‘yan kasar da gaske muke, sannan ita gwamnatin abin da ya kamata take yi? Ya ce  ya taba zama kansila kuma gwargwado ya ga yadda aka gudanar da abubuwa, kawai ana fitar da kudaden jama’a ana kashe su a kan shan shayi da yawo a motoci amma ba wai wani cigaba kasa ke samu ba.

Yana mai cewa, idan ma an zauna an tattauna su wane ne za su amince da shawarwarin a majalisar, ya ce a saninsa babban abin da zai gyara fasalin kasar nan shi ne tsoron Allah da gaskiya da amana idan an samu wadnnan lallai Nijeriya za ta gyaru, gwamnonin jahohi ba za su taba sakar wa kananan hukumomi mara ba saboda son zuciya irin nasu, su kuma shugabannin kananan hukumomi ba za su iya zama da jama’arsu ba saboda ba su da abin bayarwa.

Idan majalisa da gaske take, sun fita waje dan karo ilimi da jin bayanai game da yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati, ya ce bai ga dalilin sai irin wannan ne in ya taso ake bin talakawa ba amma lokacin da ake zabtare kudaden jama’a da sunan kwangiloli ba a neman ra’ayin jama’a, majalisa ta samar da doka ta gaskiya duk wanda aka samu da laifin rashawa a fito bainar jama’a a hukunta shi a gani idan wani zai kwatanta hakan.

“Saboda a cikin wadannan kudurce-kudurcen sha uku wanne ne APC ba ta yi wa jama’a alkawarin aiwatar da shi ba, saboda maganar gyaran fasalin kasa bai da wani fa’ida illa kawai wata hanya ce ta azurta wasu da kudin jama’a, babban mataki dai a samar da doka kuma ta fara aiki nan take a kan masu rashawa, sannan komai girman mutum idan aka kama shi da laifi a hukunta shi, kowace shiyya da irin arzikin da Allah ya ba ta gwamnati ta lalubo hanyar da kowace shiyya za ta amfana da arzikin da ta mallaka, wajen rabon a daina fifita wasu a kan wasu, a bai wa gwamnatocin jihohi damar mallakar arzikinsu ta yadda za su iya sarrafawa don amfanar jama’arsu, domin karfin da aka bai wa Gwamnatin Tarayya ya yi yawa kuma shi yasa su kansu kananan hukumomi jihohin kan tauye su domin mai dokar barci ne ya buge da gyangyadi”, in ji Hon. Dauda.

Exit mobile version