CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Kare Hakkokin Jama’a A Bangaren Masakun Jihar

by CRI Hausa
February 1, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Jihar Xinjiang Ta Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Kare Hakkokin Jama’a A Bangaren Masakun Jihar
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Jihar Xinjiang ta Uygur, mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta wallafa wani rahoton kare hakkokin jama’a a bangaren masakun jihar, wanda ya gabatar da tarihi da ci gaban bangaren da kuma muhimmancinsa ga rayuwar jama’a.

Kungiyar masu masaku ta Xinjiang ce ta fitar da rahoton, da zummar fayyace gaskiya da gina kafofin tuntuba tsakanin Sinawa da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, bisa manufofin bai daya da moriyar juna.


Bayan shekaru 70 da kafuwarsa, bangaren masakun Xinjiang, ya zama mai muhimmanci ga al’ummun dukkan kabilu a yankin, da ma masaku da masana’antun samar da tufafi na kasar Sin da duniya baki daya.
Bangaren ya samu gagarumin ci gaba wajen samar da ayyukan yi da kara kudin shigar manoma da bada gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin jihar da ma inganta rayuwar jama’arta.
Shekara 33.7 ne matsakaicin shekarar ma’aikaci a bangaren. Dukkan ma’aikatan da aka zanta da su cikin rahoton, sun ce sai da sassan kula da ma’aikata suka duba katunansu na shaidar dan kansa, domin tabbatar da shekarunsu ba su gaza 16 ba, wadda ita ce shekara mafi karanci ta aiki da dokar kwadago ta kasar ta tanada.
Dukkan kamfanoni 26 da aka nazarta cikin rahoton, na da wurin cin abinci na halal, kuma suna bayar da nau’ikan abincin kananan kabilu domin cimma bukatun ma’aikata daga dukkan kabilu.
Kamfanonin masaku a Xinjiang, na aiwatar da tsarin biyan albashi daidai da aikin da ma’aikaci ya yi, kana sun haramta wariyar jinsi. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)

SendShareTweetShare
Previous Post

An Bukaci Al’ummar Sin Da Su Yi Bikin Bazara A Wuraren Da Suke Aiki

Next Post

Wane Albishir Kamfanonin Sin Ke Yiwa Duniya Game Da Samun Rigakafi?

RelatedPosts

Sin Ba Ta Son Yin Babakere, Mutunta Juna Da Hadin Kai Sune Ginshikan Makomar Huldar Sin Da Amurka

Sin Ba Ta Son Yin Babakere, Mutunta Juna Da Hadin Kai Sune Ginshikan Makomar Huldar Sin Da Amurka

by CRI Hausa
9 hours ago
0

Daga Amina Xu Kwanan baya, farfesa jami’ar Harvard Joseph S....

Karya Ba Za Ta Boye Nasarorin Da Aka Cimma Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam A Xinjiang Ba

Karya Ba Za Ta Boye Nasarorin Da Aka Cimma Wajen Tabbatar Da Hakkin Dan Adam A Xinjiang Ba

by CRI Hausa
9 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwanan nan ne kasar Amurka da sauran...

Wang Yi: Taimakawa Kasashen Afirka Yaki Da COVID-19 Da Farfado Da Tattalin Arzikinsu Abu Ne Mafi Muhimmanci Ga Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka

Wang Yi: Taimakawa Kasashen Afirka Yaki Da COVID-19 Da Farfado Da Tattalin Arzikinsu Abu Ne Mafi Muhimmanci Ga Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka

by CRI Hausa
9 hours ago
0

Daga CRI Hausa Memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan...

Next Post
Wane Albishir Kamfanonin Sin Ke Yiwa Duniya Game Da Samun Rigakafi?

Wane Albishir Kamfanonin Sin Ke Yiwa Duniya Game Da Samun Rigakafi?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version