Jihar Yobe Na Sahun Gaba A Yawaitar Masu Luwadi –Alhaji Bukar Modu

Muhammad Sani Chinade, Damaturu.

An bayyana cewar, jihar Yobe ce ta biyu a cikin jerin jihohohin kasar nan da aka fi aikata munanan ayyukan nan na luwadi da madugo wandahakan ya haifar da yawaitar masu aikata irin wadannan ayyuka na fasadi musamman a tsakankanin matasa wadanda su ne jigon duk wataal’umma.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin tsohon babban sakatare a ma’aiktar kula da addini a Jahar Yobe, Alhaji Bukar Modu Jimbam, yayin da yakegabatar da jawabinsa a wajen bikin bita na kwana biyu da kwamitin matasa masu da’awa na kungiyar JIBWIS suka gabatar a karshen makon da ya gabata, amasallcin jumu’a na cibiyar kula da addinin musulunci na jiha da ke garin Damaturu.

Tsohon babban sakataren ya kara da cewar,wannan kiyasi na cewar, a saninsa bada dadewa ba jihar Yobe ce ta biyu a dukan jahohin kasar nanda aka samun yawaitar masu aikata wannan babbar kaba’ira, a gaskiya babban abin bakin ciki ne da takaici wanda ya zama wajibi wannankwamitin matasa masu da’awa ya tashi wurjanjan don yin kira gami da fadakarwa, ba wai ga matasa kawai ba har ma ga dukannin al’umma maza damata dangane da illar aikata wannan babban laifi a wajen Allah (SWT).

Alhaji Bukar Modu Jimbam ya ci gaba da cewar, wannan lamari babban kalubale ne da ke gaban mu musamman yadda matasa ke afkawa ga tarkonda Yahudu da Nasara ke kafa musu , yadda ya kawo wani misali a jawabin da wani tsohon Firayi ministan kasar Yahudawan Isra’ila Sheman Peref  ya taba fada kan matasan kasar nan da cewar, matasa ne masu kokarin tsoron Allah sai dai kuma suna da kishin addinansu wadda ganin hakanne suka yi kokarin ganin sun nisanta matasan da Allah suka cuso musu koyi da aikata mugayen kaba’irai da nufin zama wani abu a duniya don

cimkma burinsu na halakar da su.

Shi ma da yake jawabi a wannan biki, shugaban taron, Ustaz Babagana Malam Kyari, bayyana farin cikinsa, ya yi dangane da wannan aiki na da’awah da wadannan matasa suka dukufa yi, yadda ya kiraye su da kar su yi kasa a gwiwa dangane da wannan aiki na wa’azi ga al’umma.

Ya kara da cewar, su tuna a halin da ake ciki suna da jan aikin fadakar da matasa kan su bada gudummowarsu kan ci gaban addinin musulinci musamman ganin cewar akwai hanyoyi masu saukin bi don yi da’awah kamar shafin dandalin ganawa da abokai (Facebook) da twitter

da youtube da whatapp da sauran hanyoyin sadarwa na zamani da ba a ambata ba.

Malamin ya kuma nuna takaicinsa dangane da bayanin da aka yi na kan cewar,  wai jihar Yobe ce ta biyu bayan jihar Kano da ke da yawan mutanenda su ka fi yawan aikata munanan fasadin nan na luwadi da madugo wadda a cewarsa  wannan labarin abin tir ne.

Don haka, ya kira matasa wadanda suke da kusan kashi kusan 85 na dukannin al’umma da kuma wasu daga cikin manya-manyan mutanen da kejagorantar matasan don aikata wannan fasadi da zimmar biyan wadansu bukatunsu na duniya wasu bokaye ke dora su akai da su ji tsoron Allah

ta wajen gujewa ci gaba da aikata hakan, su tuna cewar, wannan jiha ba ta  jima da fara farfadowa ba daga iftila’in da Allah (SWT) ya kawo na Boko-Haram, to sai ga shi ana kokarim takalar Allah (SWT) wajen aikata wadannan laifuffuka tsakanin maza da maza da kuma mata da mata.

To wallahi muddin lamarin ya ci gaba to kuwa abubuwan da za su biyo baya kan dara na baya Allah Ya saukaka.

Exit mobile version