Connect with us

MANYAN LABARAI

Jihar Yobe Ta Amince Da Daurin Rai-Da-Rai Ga Masu Aikata Laifin Fyade

Published

on

Gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam ya rattaba hannu akan dokar daurin rai-da-rai da kuma shekaru 25 ga duk wanda aka samu da laifin fyade ga manya ko yara kanana.

Gwamnan ya ce; matakin da gwamnati za ta dauka akan masu aikata munanan laifukka irin su fyade da garkuwa da mutane da sauran laifinka da suke da muni, zai taimaka matuka wajen dakile laifukkan a fadin kasar nan.

‘Duk wanda aka samu ya aikata laifin fyade akan karamar yarinya ko yaro, toh hukuncin shi daurin rai-da-rai ne, in kuma laifin yi wa babba fyade ne to hukuncin daurin shekaru 25 ne a gidan kaso.’ Inji Geidam

Geidam ya kara da cewa; in aka samu mutum da laifin yin garkuwa da mutane, toh zai fuskacin daurin shekaru 14 a gidan yari, don haka duk wanda ya yi wata mu’amalar aure da ya shafi tursasa wani, mace ko namiji, zai iya fuskantar daurin shekaru 25 ko shekaru 14.

Doka ta tanadar da hukunci ga duk wanda dauke wani, ko ya yaudare shi don ya bi shi wani waje, ko kilace shi ba bisa ka’ida ba, ko kuma ma ya mishi barazana don ya bishi wani waje ba a son ranshi ba, toh wannan zai fuskanci hukuncin mai yin garkuwa da mutum, wanda dauri ne.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: