Jihar Yobe Ta Gina Dakin Musamman Na Kula Da Yara A Asibitin Potiskum Da Gashua

Daga Bello Hamza, Abuja

Kwamishinann lafiya na jihar Yobe, Dr Mohammad Gana, ya sanar da cewa, jihar ta kashe fiye da Naira Miliyan 72 wajen ginawa tare da sake fasalin dakin kula da yara na musamman a asibitin kwararru na garin Potiskum da Gashua.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a taron manema labarai na bikin cika shekara 2 da mulkin Gwamna Mala Mala-Buni a matsayin Gwamna jihar.

Ya kuma ce, an tura Likitoci da Nas-nas 10 asibitin Reddington Group da ke Legas don a horas da su sanin yadda za su kula da sashin kula da yara na asibitocin da aka kafa a garin Damaturu.

Ya kuma ce, an kashe fiye da Naira Miliyan wajen samar da kayan aiki na zamani a asibitin garin Damaturu da kuma manyan asibitocin jihar da ke garin Potiskum, Gashua, Geidam da kuma Buni-Yadi inda aka daga darajarsu zuwa asibitn kwararru.

Ya ce, an samar da kayan aiki na zamani wadanda suka yi daidai da abin da ke samu a sassan duniya.

Ya kuma bayyana cewa, wadannan na daga cikin nasarorin da gwmnatin yobe ta samu a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.

 

 

 

Exit mobile version