Jihar Yobe Ta Jaddada Aniyarta Na Samar Da Cikakken Kiwon Lafiya Ga Al’ummarta

Buni Yobe

Daga Bello Hamza,

Gwamnatin jihar Yobe ta kara jaddada aniyarta na samar da cikakken tsarin kiwon lafiya ga al’ummar jiihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Lawan Gana, ya bayyana haka ranar Asabar a garin Kano a taron kwanaki uku da hukumar ‘Contributory Health Care Management Agency’ ta jihar Yobe ta shirya don lura da irin tsarin da aka shiya na samar da tsarin inshora ga al’ummar jihar.

Ya ce, samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga al’ummar jihar wani bangare ne da Gwamnan jihar Gob. Mala Buni ya ba mahimmanci a mulkinsa.

Ya kuma ce, “Burinmu shi ne na ganin yawancin al’ummar mu na samun ingantaccen kiwon lafiya kuma a cikin sauki nan da shekarar 2030.”

Kwamishinan ya kuma ce zuwa yanzu hukumar ta yi rajistar ma’aikata 200,000 cikin tsrain inshora na jihar.

Ya kumn lura da cewa, gwamnati ta ware kashi 1 na kudaden da take samu daga gwamnatin tarayya don biya wa marasa karfi nasu kason ga tsarin fanshon kiwon lafiyar.

Ya kuma bukaci masu halartar taron su jajirce wajen fito da tsrain da zai taimaka wa al’umma jihar, tsarin da zai fadakar da al’umma jihar wajen kawo kansu a cikin tsrain ba tare da wani matsala ba.

Exit mobile version