Daga Hussaini Yero,
A jiya ne gwamnatin jihar Zamfara ta karbi allurar rigakafin Korona guda 55, 920 daga gwamnatin Tarayya.
Jagoran amso allurar rigakafin, kwamishinan lafiya na jihar zamfara, Alhaji Yahaya Muhammed Kanoma, ya bayyana cewa, gwamnati zata tsaya tsayin daka domin taga ko wane van jihar anyi masa wannan allurar rigakafin.
“Kwamishina Kanoma, ya bayyana cewa, akaron farko mutanene da sama ne za su karvi alluran a jihar, kuma matakin allurar rigakafin ne tun daga ‘yan shekaru 18 zuwa sama ne za’ayi ma allurar a fadin jihar, inji Kwamishinan.
Hon Kanoma ya bayyana mutanen da za su fara karbar allurar rigakafin cutar za su kasance masu fada a jiya bayan an kammala yima gwamna Bello Matawalle Maradun da manyan mukarraban gwamnati, daga nan sai ma’aikatan lafiya, sarakunan gargajiya, da masu sayar da man fetur ‘yan jarida da sauran su.
Kuma yanzu haka wasu likitocin suna karbar horo kan yadda za a ba da rigakafin da zarar an kammala horon za su fara aikinsu.
Kwamishinan ya yaba wa hukumomin UNICEF da WHO kan kokarin da suke yi na tabbatar da allurar rigakafin ta isa Jihar ta Zamfara.
Kuma munyi kyakkyawan shiri don adana alluran ta hanyar tabbatar da wadatar ciyar wutar lantarki tare da kara dakunan sanyi masu awanni 24, tare da wutar lantarki da injunan samar da wutar lantarki guda biyu da kuma makamashin hasken rana.