A gobe Alhamis ne gwamnonin Arewa Maso Gabas za su hallara a jihar Gombe domin tattauna muhimman batutuwa masu alfanu da suka jibinci rayuwar al’ummominsu ciki kuwa har da matsalolin tsaro da na hasken wutar lantarki domin wa tufkan hanci warwara.
Gwamnonin da za su hallara a Gomben sun hada da, Bala Muhammad na jihar Bauchi; Ahmadu Umaru Fintiri gwamnan Adamawa; Mai Mala Buni gwamnan jihar Yobe; Darius Dickson Ishaku gwamnan jihar Taraba; Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno da kuma shi kanshi Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Bayanin ganawar tana kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Ismaila Uba Misilli, babban mai taimaka wa gwamnan jihar Gombe kan hulda da ‘yan jarida ya fitar a yammacin yau din nan gami da aiko da kwafinta wa LEADERSHIP A YAU, yana mai cewa irin wannan taron ganawar shine irinsa na farko, ya kara da cewa gwaman Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ne zai kasance mai masaukin baki.
Ya ce, za su gana ne kan muhimman batutuwa da suka shafi shiyyar arewa maso gabas da suka hada da suka shafi matsalolin tsaro, tattalin arziki da kuma shimfida ababen more rayuwa a tsakanin al’umominsu.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnonin za kuma su tattauna kan lamarin da ya shafi samun albarkatun danyen mai a shiyyar arewa maso gabas da kuma sauran batutuwan da suka shafi sha’anin wutar lantarki hadi da kuma dokar Discos.
Har-ila-yau, gwamnonin za kuma su amshi rahoto daga wajen hukumar bunkasa shiyyar arewa maso gabas (NEDC) kan binciken hukumar na bunkasawa da kyautata rayuwar jama’an shiyyar.
Ganawar na tsawon kwana guda ana sa ran zai fitar da wani wani dandamali na tattaunawa a tsakanin gwamnonin shiyyar domin tsarawa da fitar da matakan da suka dace na kula da rayuwan al’ummomin yankunansu.
A karshen taron gwamnonin za su fitar da bayanin bayan taro da batutuwan da suka kai ga tsaida matsaya a kansu, gwamonin arewa maso gabas din da za su yi ganawar sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe da na jihar Taraba.