Daga Bello Hamza
Alhaji Hassan Ɗanbaba shi ne na biyu daga cikin manayan masu naɗi a Majalisar Sarkin Musulmi, kuma na uku a cikin jerin muƙaman sarautar Majalisar, a yau Allah ya albarkace shi da cika shekara ashirin a matsayin Magajin Garin Sakkwato.
Hassan Danbaba, ya gaji Magajin Garin Sakkwato, Abubakar Danjada, kuma shi yana matsayin ɗa a wajen Magajin Garin, Aliyu, wanda ya hau karagar mulkin bayansa. Alhaji Hassan Ɗanbaba ne ya fara riƙe sarautar Katukan Sakkwato, kafin naɗa shi a mtsayin Magajin Garin Sakkwato na 13 ranar 31, Oktoba, a shekara ta 1997.
Kamr yadda tarihin Daular Sakkwato ya nuna, Magajin Garin Abubakar Danyada, shi ne ma fi kusaci, kuma mai bai wa Sarkin Muslmi Muhammadu Bello,shawara, saboda haka ne ma aka naɗa shi Magajin Garin na farko a shekara ta 1803, bayan kafa Daula.
Alhaji Hassan Danbaba, wanda Allah ya albarkace shi da basirar yadda zai gadanar da dukkan al’amarin da ya zo gabansa yadda za a samu nasara, hakan ta ƙara fito wa fili saboda nasarorin da ya samu a tsawon shekara ashirin da ya yi, a matsayin Magajin Garin Sakkwato, ya kuma bayar da cikakkiyar gudummawa wajen ci gaban Majalisar Sarkin Musulmi a wannan matsayi nasa. Yana riƙe da matsayin matimakin shugaban kwamitin masu zaɓen ‘yan Majalisar Sarkin Musulmi, kuma shi ne shugaban kwamitin kuɗi da wasu abubuwa na Majalisar Sarkin Musulmi. Alhaji Hassan Ɗanbaba mamba ne ha Hukumar gudanarwar Jami’ar Usmanu Danfodiyo, kuma matimaki na musamman ga tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan masarautu.
Hamshaƙin ɗan kasuwa ne mai taimakon jama’a, Magajin Garin Sakkwato mutum ne da ya ba al’umma gudummawa a fannin rayuwa daban-daban a ko’ina cikin faɗin ƙasar nan, waɗanda suka zame masa Sadaƙatal jariya.
Daga cikin irin waɗannan gudummawar akwai; bayar da tallafin karatu a fagage daba-daban, sannan kuma ya gina makarantun islamiyya da masallatai da rijiyoyin burtsatse ga al’umma a ko’ina cikin faɗin ƙasar nan.
Alhaji Hassan Ɗanbaba shi ne na biyu daga cikin manayan masu naɗi a Majalisar Sarkin Musulmi, kuma na uku a cikin jerin muƙaman sarautar Majalisar, a yau Allah ya albarkace shi da cika shekara ashirin a matsayin Magajin Garin Sakkwato.
Hassan Danbaba, ya gaji Magajin Garin Sakkwato, Abubakar Danjada, kuma shi yana matsayin ɗa a wajen Magajin Garin, Aliyu, wanda ya hau karagar mulkin bayansa. Alhaji Hassan Ɗanbaba ne ya fara riƙe sarautar Katukan Sakkwato, kafin naɗa shi a mtsayin Magajin Garin Sakkwato na 13 ranar 31, Oktoba, a shekara ta 1997.
Kamar yadda tarihin Daular Sakkwato ya nuna, Magajin Garin Abubakar Danyada, shi ne ma fi kusaci, kuma mai bai wa Sarkin Muslmi Muhammadu Bello,shawara, saboda haka ne ma aka naɗa shi Magajin Garin na farko a shekara ta 1803, bayan kafa Daula.