Connect with us

Ka San Jikinka

Jikin Mutum Lokacin Sanyi

Published

on

’Yan uwa masu karatu, assalam alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake saduwa a wannan shafi da ke zakulo mu ku bayanai game da jikin dan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. A yi min afuwa na shiru da a ka ji, hakan ya faru ne sakamakon tarin karatu da ya yi min yawa. Amma yanzu Alhamdulillah!
Duba da lokacin da muke ciki yanzu, rubutun yau zai mayar da hankali wajen bayani akan yadda jikin dan adam ke gudanar da al’amuransa lokacin sanyi; da kuma shawarwari kan yadda mutum ya kamata ya kula da kansa a wannan yanayi. Idan kun shirya, bismilla.

A duk lokacin da yanayi ya canza, to shima jikin dan adam ya na canzawa, domin tafiya da wannan yanayi ta yadda jikin ba zai cutu ba. Watakila mafi yawan mutane abinda su ka fi sani shi ne sanyi na damun su a hannu da kafafu; kunnuwansu da idanunsu. Fiye da haka, jikinka da nawa ya na jin sanyi kuma ya na daukar matakai na rage jin sanyin. Amma ba kowa ne yasan hakan ba.

 

Da farko ma, ya ma ake kasan kana jin sanyi?

Jin sanyi yana faruwa ne a lokacin da jijiyoyin laaka da suke damfare a jikin fata suka fahimci cewa iskar sanyi ta bugi fata. Daga nan sai su dauki sako izuwa kwakwalwa cewa: “sanyi fa ya bugi fatar jiki”; to daga nan sai kwakwalwa ta fassara sakon da cewa sanyi ya sauka akan fatar, tare da aiko umarnin hukunci da ya kamata a dauka: shin bargo zaki rufa? Ko rigar sanyi zaka sanya? Ko hancinka zaka toshe?

Kwakwalwar ka ta na daukar matakai na ciki da na waje domin kare ka/ki daga illolin sanyi. Matakai na waje sun hadar da rufe kofa da tagogi, sanya riguna jibga-jibga masu rage shigar sanyi cikin jikinmu da kuma samar mana da dumi, sanya safa ta hannu da ta kafa, da sauransu.

Idan ku kayi tunani, su kansu wadannan matakai da muke ganin cewa na waje ne, sun samo asali ne daga sassa guda biyu na kwakwalwa: daya ana ce masa “cerebral corted”, dayan kuma ana ce masa “limbic system”. Hadin gwuiwar wadannan sassan guda biyu na kwakwalwa shi ne ke fayyace irin sanyin da zamu ji.

“Cerebral corted” cibiya ce mai sarrafa hankalin dan adam; “Limbic system” kuwa cibiya ce ta da ke kula da yadda muke jin yanayin jikinmu (misali murna, fushi, jin zafi, ko jin sanyi, da sauransu).

Yadda wadannan cibiyoyi suka fassara abin ke fuskantarmu, haka halayyarmu za ta kasance. Idan wani zai daure ya fita a cikin muku-mukun sanyi izuwa shago ko ofis, cibiyoyin nan guda biyu su ne a bakin aiki. Ku kalli mahaukaci mana, da yake cibiyar hankali dake kwakwalwarsa bata aiki, sai kuga yana ta yawo cikin sanyi abinsa.
Yanzu bari muga matakai na ciki. Babban matakin da jiki ke dauka shi ne taskance zafin jiki domin a dumama shi kada sanyin gari yayi masa illa. Akwai hanyoyi da matakai da jiki ke dauka wajen taskance zafin da ke cikin jiki.

Jikinka zai rage yawan jinin da ke zuwa sassan daban daban na jiki ta hanyar tsuke jijiyoyin da jini ke gudana. Hanyoyin jini da ke kasan fatarki ko fatarka suna dauke da jini mai dumi ne. A tsarin aikin jikin dan adam, wannan dumi da jinin ke dauke da shi, da zarar ya kusanci fata sai dumin ya sirare ya fita da hudojin gashi dake fata, tare da gumi.

To a lokacin sanyi, jikinmu yana son wannan dumi da jinin ke dauke da shi, saboda haka sai jiki ya yi kokarin rage yawan jinin da ke biyowa hanyoyin jini na karkashin fatarka. Ana farawa ne ta kan jijiyoyin jinin da ke karkashin fatar hannaye, da ‘yan yatsu, da kuma kafafu da yatsunta.

Tunda jini mai dumi ya rage zuwa karkashin fatar hannu da ta kafa, hakan sai yasa mu dinga jin sanyi a hannayenmu da kafafuwanmu fiye da sauran sassan jiki.

A dunkule, shi jikin mutum kamar mashin yake; yayin da sanyi ya busa, yanayin dumama ko zafin gari ya ragu, sai jiki ya ririta dumin da yake dashi a wannan yanayi.
Kwakwalwarka za ta dinga angiza tsokar jikin mutum ta dinga motsawa da sauri sauri. Wannan shi ake kira rawar dari.

Amfanin hakan shi ne samar da zafi wanda zai dumama jiki. A duk sanda wata gaba ke aiki a jikin mutum, to zafi na samuwa ta ciki; kamar yadda idan ka kunna wata na’ura zafi zai samu. Wannan yawan mammotsawar tsoka da sauri lokacin da mutum ke rawar dari itace hanyar da jiki ke samarwa da kansa dumi.

Kenan ashe jikin mutum yana aiki iri biyu anan: Alkinta dumin jiki, da kuma samar da dumin jiki. Wannan wata rahama ce daga Rabbul Izzati. Domin kulawa don kada dumin da ke cikin jiki yayi kasa, akwai ‘yan aike masu matukar saurin fahimtar sauyin yanayi dake karkashin fatarka: idan an mintsineka, ko an yakusheka, ko ka taka wani abu, da sauri zasu sanar da kwakwalwa cewa ga abin ke faruwa.

A yayin jin sanyi, zasu dauki sakon cewa sanyi ya bugi fata sukai izuwa ga wata halitta ko cibiya a cikin kwakwalwa mai suna” hypothalamus”. Wannan cibiya itace mai daidaita dumin jikina da naki da naka; idan dumin yayi kasa sai ta kara; idan kuma yayi yawa sai ta rage.

Haka kuma, wasu lokutan musamman idan muka shaki iska lokacin sanyi, mukan ga hancinmu yana yoyyon majina; me ya sa?

Jikin dan adam kullum cikin kokarin kare mutum yake daga cuta. Saboda haka a kokarin jiki na kare shigar cututtuka ta hanyar iskar da muke shaka, yasa majina ke fita daga hancinmu.

Yadda abin yake shi ne: a cikin iska akwai da datti da kura iri-iri. To da zarar mun shaki irin wannan iskar,  kwayoyin halitta dake damfare a bututun iska da makogwaro zasu gane cewa ka shaki gurbatacciyar iska. Nan da nan bututun iska, wanda ya fara daga kofofin hanci zuwa cikin huhu, sai ya fara samar da majina.

Amfanin majinar shi ne tarfa datti da kurar da ke cikin iska wadda zata iya lahani ga jikin dan adam. Idan akwai cutuka da yawa a cikin dattin da ke iska, to tabbas kwayoyin halittar da suka gina bututun iska za su samar da majina mai yawa, har ma ta fara fitowa ta hanci.

Saboda gudun kar mu yada cuta, yana da kyau mu guji fyace majina a jikikn bango dan kada wani ko wata su taba da hannunusu, sannan kuma suyi amfani da hannun wajen cin wani abu, ko yada cuta ta hanyar musabiha da wani.

Yanzu kuma bari muga hanyoyin da ya kamata mu bi domin kula da kanmu lokacin sanyi.

*Mu dinga yawan shan ruwa, saboda hakan zai taimakawa jikinmu ta fuskoki da dama kamar karawa kwayoyin halittar jikinmu kuzarin ci gaba da gudanar da ayyukansa.

*Mu dinga kula da fatarmu don kada ta bushe lokacin sanyi. Kamar yadda kuka gani, fata tana taimakawa wajen samar da dumi a jikinmu. Wanka, ko da sau daya ne, da shafa mai a jikinmu kan taimaka wajen hana bushewar fata.

*Mu dinga motsa jiki saboda hakan zai sa tsokokin jikin mu su samar da zafi ko dumi domin amfanar jikinmu lokacin sanyi.
Advertisement

labarai