An Jinjina Wa Matasan Yankin Kebbi Ta Kudu

Mataimaki Jagoran Majalisar Dattijai kuma mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu a jihar Kebbi Bala Ibn Na’Allah ya yaba wa matasan yankin mazabarsa bisa jerin gwanon da suka yi cikin  lumana don nuna rashin amincewarsu a kan ayyuka marasa inganci da aka yi a yankin.

Matasa daga yankin karamar hukumar Zuru sun gudanar da jerin gwanon ne don nuna rashin amincewarsu da wasu aiyuka marasa inganci da aka gudanar a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Zuru “Federal Technical College, Zuru”.

Dan Majalisar Ya ce, gwamnatin tarayya za ta amfana matuka in aka bar ‘yan majalisa su rinka lura da yadda ake gudanar da ayyuka a hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya a mazabarsu. Ya nuna takaicinsa na cewa, duk da kokarin da yake yi na kawo ayyukan ci gaba daga hukumomin gwamnatin tarayya mazabarsa “Sau da yawa sai a bai wa wadanda ba su da kwarewar da ya kamata kwangilar aiwatar da ayyukan”

“Abin da ke faruwa a Kwalejin Kimiyya da ke Zuru lallai abin takaici ne, duk da dimbim kudaden da gwamnati ta zuba babu wani abin a zo a gani, zan gabatar da lamarin ga Ma’aikatan Kula da Muhalli ta kasa domin ta kawo dauki” in ji shi.

Sanata Na’Allah ya kuma bukaci matasa da su ci gaba da kalubalantar duk wani shiri na gwamnati da ba su aminta da shi ba cikin lumana ta yadda aiyukan da gwamnati ke gudanarwa a za su anfani jama’ar da aka yi dominsu.

“Wannan kuma na nuna irin ci gaba da aka samu na wayewa a tsakanin matasan yankin Kebbi ta kudu, na yi murna matuka” in ji shi.

Exit mobile version