Jinjina Wa Shekau Ta Jefa Mai Taimaka Wa Dan Majalisa Jangwam A Borno 

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

dan majalisa mai wakiklar cikin kwaryar Maiduguri a zauren majalisar wakilai, Hon. Abdulkadir Rahis, ya dakatar da mai taimaka masa, Bukar Kurama, wanda aka fi sani da Tanda, saboda yadda ya fito fili ya jinjina wa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, tare da bayyana shi a matsayin “hakikanin gwarzo” saboda yadda ya ki ya mika wuya a gumurzun da ya barke tsakaninsu.

Mai taimaka wa dan majalisar, Tanda, ya yi wannan furucin ne a shafinsa na Facebook ranar Alhamis da ta gabata domin bayyana ra’ayinsa, inda ya rubuta: “ya yi matukar burge ni, abin a yaba (Shekau) abin da ya karfafa gwiwa a rayuwa har zuwa karshen rayuwarsa. Ya rayu irin ta gwaraza kuma ya mutu a matsayin gwarzo, wanda ta kai an rasa gano inda gawarsa take.”

Kan ka ce me, kalaman Tanda sun daga hankula ciki har da jami’an tsaro, wanda ya jawo jama’a da dama suka zarge shi da ra’ayin nuna goyon baya ga mayakan Boko Haram wadanda hare-haren su ya jawo mutuwar dubun-dubatar jama’a a yankin kama daga 2009 zuwa yau, tare da tilasta garuruwa bila adadin kaura zuwa matsugunan yan gudun hijira a arewa maso gabas.

Bugu da kari, jim kadan da faruwar wannan lamarin, Hon. Rahis ya sallami Bukar Tanda ta hanyar takardar dakatarwa wadda aka raba wa manema labarai ranar Lahadi a birnin Maiduguri, tare da shaidar da cewa wannan katobara da Tanda ya furuta ra’ayinsa ne wanda ya yi hannun riga da na dan majalisar wakilan, jam’iyyar APC da al’ummar mazabar.

Wanda a sanarwar ya bayyana cewa, “Na rubuta daukar wannan matakin a hukumance don in sanar maka cewa na suke ka daga matsayinka na mai taimaka wa dan majalisa.”

“Wannan mataki naka, furucin da kayi a matsayin ra’ayinka a yan kwanakin nan ya yi hannun riga da nawa, haka kuma ya saba da na al’ummar mazabata tare da jam’iyyar mu ta APC.”

“Har wala yau kuma, wannan wasika za ta zama shaidar mun raba gari dangane da duk wani matakin da ka dauka ko kake son ka dauka, bani da alka dashi balle kuma ofishina.”

Exit mobile version