Jiragen Ruwa 15 Dauke Da Man Fetur Sun Shigo Nijeriya

Rahotannin sun bayyana cewa, kimanin manyan jiragen ruwa sha biyar dake dauke da tataccen man fetur da sauran kayayyaki ne suka iso cikin kasar nan ta tashoshin jiragen ruwa guda biyu dake Legas.

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasar nan NPA ta sanar da cewa, tashoshin jirage ruwan sune na Apapa da na Tin Can Island dake a cikin jihar Legas. Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasar nan NPA ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis dataganata.

A cewar Hukumar ta NPA, a yanzu a haka jiragen suna jiran a fara sauke kayayyakin da suka shigo da su cikin kasar nan. NPA ta kara da cewa, daga cikin jiragen guda sha biyar, akwai guda hudu dauke da da man fetur a yayin da sauran sha daya sun yi jigilar nau’o’in kayayyaki daban daban.

Sanarwar ta Hukumar NPA ta ci gaba da cewa, akwai sauran jirage ashirn da hudu da zasu shigo cikin kasar nan, daga ranar sha biyar zuwa talatin na wannan watan.

Hukumar ta NPA ta sanar da cewa, jirage ashirin da hudu da ake jiran shogowarsu,

zasu yo dakon kayan da suka hada da, buhunhunna Sikari, Gishiri, Kifi, Fulawa, Sundukai da kuma hajoji daban-daban.

A cewar Hukumar, a yanzu haka jirage sha takwas suna sauke motoci, sundukai, hajoji, man dizil, iskar gas da kuma kifi.

 

 

Exit mobile version