Jirgin Ƙasa Ya Yi Arangama Da Motar Ɗangote Da Babur Na A Daidaita Sahu A Kano

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano.

Wani jirgin ƙasa da ya taso daga Jihar Legas ya yi taho mu gama da wata Motar Ɗangote wadda ke ɗauke da siminti tare da wani babur ɗin a daidaita sahu a titin Obasanjo da ke Kano.
Wani ganau wanda ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a kusa da titin jirgin ƙasa, ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa “mun hangi motar ɗangote  na gabatowa kusa da titin jirgin, ya yinda shi kuma jirgin ya taho a guje. Mun yi ƙoƙarin tsayar da direban babbar motar, sai dai direban bai Lura da abinda muke nuna masa ba.”
Babu tabbacin wani ya mutu a lokacin haɗarin, amma dai an garzaya da waɗanda ke cikin babur ɗin zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

 

 

Exit mobile version