Wani abin alhini ya faru a yankin Masarautar Jere yayin da jirgin kasan da ke jigilar injiniyoyi masu aikin gyara layin dogo na Kaduna-Abuja ya halaka dabbobin da akalla yawansu bai gaza 700 ba.
- ‘Yan Bindiga Sun Saki Sabon Hoton Fasinjojin Jirgin Kasa Kaduna Da Aka Sace
- Karuwar ‘Yan Takarar APC: Kallo Ya Koma Kan Buhari
- 2023: Buhari Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tinubu A Fadarsa Da Ke Abuja
Al’amarin wanda ya faru a daidai kasan gadar Azara, ya auku ne a yau Juma’a da misalin karfe 11:30 na safe.

Majiyarmu daga Babban Ofishin ‘Yansanda (Area Command) na Jere ta tabbatar da cewa, daga cikin dabbobin da jirgin ya halaka akwai tumaki, awaki har da jakuna.
Majiyar ta kara da cewa, “Wannan Hatsarin jirgin kasan ya faru ne inda ya rutsa da tumaki, awaki, jakuna da misalin 11:30am yau (Juma’a) a gadar Azara da ke yankin Masarautar Jere a Karamar Hukumar Kagarko cikin Jihar Kaduna.”

Da aka tambayi majiyar ko me ya haddasa hatsarin, ta ce “sakamakon rashin hanyar tsallaka kogin Azara da ba a yi wa mutane da dabbobi ba don su rika samu suna tsallakawa musamman idan kogin ya kawo ruwa sai suka bi ta hanyar jirgin bisa tunanin cewa jirgin bai dawo aiki ba tun bayan harin da aka kai masa ranar 6 ga Mayun 2022.
“Jirgin kasan yana daukar ma’aikata masu Maintenance (gyara) ne. Yau (Juma’a) ya taso daga Abuja zuwa Kaduna shi ne wannan tsautsayin ya faru. Dabbobi ne na wasu Fulani. Area Commander na ‘yansanda da kansa ya ziyarci wurin bisa rakiyar wasu jami’ansa don tantance abin da ya faru. Gaskiya abin babu dadi wallahi.” In ji majiyar tamu.