Wani jirgin kasa ya yi karo da wata babbar mota makare da abincin dabbobi a mararrabar ‘Jonathan Coker Railway Lebel’ a yankin Fagba na Iju Ishaga da ke jihar Legas.
Hatsarin ya auku ne da misalin karfe tara na safiyar ranar Litinin 15 ga Fabrairu, 2021.
An tunanin cewa mutane da dama sun ji raunin a yayin hatsarin.
Yanzu haka jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa da jami’an tsaro suna wurin da hatsarin ya faru don tabbatar wucewar ababen hawa cikin sauki da kuma dakile duk wani hadarin da ka iya aukuwa.
Hatsarin ya haifar da tushewar zirga-zirgar ababen hawa a kan hanyoyin shiga yankin.