Connect with us

LABARAI

Jirgin Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Hatsari A Kasar Mali

Published

on

Jirgi mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wata mummunar sauka a wuyace a filin jirgin sama na Gao da ke gabashin Mali, in ji Majalisar. Inda mutum 11 suka jikkata ciki harda jami’an Majalisar na musamman.

Jirgin ya taso ne daga birnin Bamako da safiyar jiya Litinin dauke da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya hudu da kuma ma’aikatan jirgin bakwai.

Majalisar ta ce Jirgin yayi mummunar lalacewa. Amma ta ce za a yi bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Advertisement

labarai