Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma’a ne farkon matsakaicin jirgin ruwan yaki dankon jirage masu saukar ungulu na yaki samfurin 076 na kasar Sin, wato jirgin ruwa na Sichuan, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta kamfanin kera jiragen ruwa na Hudong-Zhonghua a Shanghai, zuwa wani yankin teku don gudanar da gwajin sufuri a karon farko. Gwajin sufurin a kan teku, zai mayar da hankali ne kan tabbatar da ingancin tsarin motsi, da sarrafa wutar lantarkin jirgin ruwan na Sichuan.
An bayyana cewa, tun lokacin da aka sanya jirgin cikin ruwa a watan Disamban shekarar 2024, an ci gaba da ginin jirgin ruwan na Sichuan bisa tsari, an kuma kammala gwajin tsayawa, da kuma daidaita kayan aiki, wanda ya ba da damar fara gwajin zirga-zirgarsa a cikin teku. (Amina Xu)












