Bello Hamza" />

Jirgin Yakin Neman Zaben Saraki Ya Isa Arewacin Nijeriya

A shirye shirye kaddamar ya yakin neman zaben shugabancin kasar nan da Shugaban Majalisar Dattijai Dakta Abubakar Bukola Saraki ke shirin yi a  yankin Arewa maso Kudu da kuma Arewa  maso Gabashin kasar nan, tawagar jirgin yakin neman zaben ya isa yankin don tataunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP don tsara yadda Saraki zai samu nasarar zama dan takarar shugabancin kasar nan daga jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Tawagar na karkashin jagoramcin Sanata Ubali Shittu (Arewa Maso Yamma) da Sanata Isa Hamma Misau (Arewa maso Gabas), ana sa ran za su tattauna da ‘yan siyasa a yankunan, a na sa ran Shugaban Majalisar,  Bukola Saraki zai jagoranci wata babbar tawaga ta manyan ‘yan siyasa daga yankuna don kokarin neman amincewar  jam’iyyar PDP a zaben fid da gwani da za a gudanar, tawagar za ta kunshi Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai da Tsaffin gwamnoni don neman amincewar wakilan jam’iyar a zaben fid da gwani da za a gudanar ranar 6 ga watan Oktoba 2018 a babban taron ja’iyyar.

A ranar alhamis ne Shugaban Majalisar Dattijan ya karbi takaradar bukatar neman takarar shugabancin kasar nan a karashin jam’iyyar PDP a ofishinsu dake Abuja. Kafin siyan takardar sai da Shugaban Majalisar ya tattauna da gwamnoni 9, cikinsu a kwai Nyesom Wike na jihar Ribas da Seriake Dickson na jihar Bayelsa da Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom sai kuma Ifeanyi Okowa na jihar Delta da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Inugu da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara sai kuma Ayodele Fayose na jihar Ekiti.

Tuni ya kuma tattauna da dattawan kasarmu, kamar tsaffin shugabanin kasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan da Ibrahim Babangida da sauransu.

Wadannan tataunawar na cikin kokarin Saraki na tabbatar da cewa, an samu fahintar dukkan masu ruwa da tsaki kafin babbar taron jami’yyar da za a gudanar a watan Oktoba na wannan shekarar.

Wakilan dake kula da yankin Arewa maso Yammacin kasar nan sun hada da Sanata Shittu da Sanata Yakubu Mohammed da mai bai wa Shugaban Majalisar Ddattijai shawara a  kan harkokin siyasa,  Alhaji Akilu Ndabawa da kuma Hajiya Fati Kamba, wata dattijiya daga jihar Kebbi sai kuma Alhaji Sheriff Hashiru, shugaban matasa daga jihar Kano.

Daga bangaren Arewa maso Gabas kuma a kwai Sanata Isah Hamma Misau da Hon. Binta Bello da Alhaji Abubakar Jada da Injiniya Mohammed Kachalla sai kuma Mista Seth Crowther. Sanarwar wannan shirye shiryen ya fito ne ta haunnu mai ba wa shugaban majakisar dattijai shawara a kan harkokin wasta labarai, Mista  Yusuph Olaniyonu.

Exit mobile version