Connect with us

SIYASA

Jirgin Yakin Neman Zaben Saraki Ya Isa Jihar Borno

Published

on

A yau Asabar 22 ga watan Satumba 2018, ne jirgin yakin neman zaben Shugaban kasa na Shugaban Majalisar Dattijai, Dakta Bukola Saraki ta isa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno domin ganawa da shugabanni da wakilan jam’iyyar PDP, a shirye shiryen da ake yi na gudanar da zaben fid da gwani na wanda zai daga tutar jami’iyyar a zaben shugaban kasa me zuwa 2019, Dakta Saraki dai na daga cikin ‘yan takara na gaba gaba daga cikin wadanda suke neman jam’iyyar PDP ta tsayar dasu takara a karkashin tutarta, tuni tawagar jirgin yakin neman zaben Dakta Saraki ta karkade yawanci jihohin kasar nan inda yake tattaunawa da shugabannin jamiyyar da wakilai a kan bukatar zabensa a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: