Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Jirgin Yakin Sojin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Katsina

Wani jirgin yakin sojin saman Nijeriya ya yi saukar gaggawa a hanyarsa ta dawowa daga yaki da ‘yan ta’adda , wanda ke gudana a yankin arewa maso yammacin kasar nan a karkashin shirin Operation Hararan Daji.
Har zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan afkuwar hatsarin wanda ya faru a jihar Katsina yau Laraba, 12 ga watan Yuni. Har ila yau rahotanni sun bayyana cewa ba’a samu rashin rai ba daga cikin mutanen da ke cikin jirgin da kuma wadanda ke kasa a lokacin da lamarin ya afku.
Shugaban Hafsan sojin sama Air Marshal Sadiq Abubakar, ya umurci sashin bincike na hukumar da tayi gaggawan bincike don gano dalilin da ya haddasa lamarin. Hukumar ta bayyana cewa tana neman tallafi da fahimtar jama’a bisa ga jajircewa da hukumar ke yi don ganin ta tsare Nijeriya da ‘yan Nijeriya baki daya
Exit mobile version