Jita-jita A Ke Yadawa Kan Mahaifina, Inji Mohammed Zakzaky

Daga Mohammed Ibraheem Zakzaky

Da safiyar nan na yi ta samun kiraye-kirayen waya daga mutane, dangane da wani jita-jita da ke yawo cewa walau jikin Mahaifina ya yi tsanani ko ya ma rasu. Domin samun tabbaci sai na nemi hukumomin gidan yarin da ake tsare da mahaifana, inda suka lamunce mana zuwa ganinsu. Ban ma wani dade da dawowa daga wurin nasu ba.

Duk da yake mahaifina yana fama da wasu cututtuka masu hatsarin gaske ga rayuwarsa, saboda raunukan da yake dauke da su, ga shi kuma a tsare a kurkuku. Bayan wannan, maganganun da ake yadawa yau jita-jita ne marar tushe.

Ina so a fahimta da kyau cewa, wannan jita-jitar an kirkireta ne da gangan da zimmar yin amfani da halin da ake ciki don haifar da rikici da fargaba. Wanda sam! Rikici da tada-zaune-tsaye ba su taba zama salon mahaifina ko na mabiyansa ba.

Exit mobile version