Jiya Aka Fara Gasar Cin Kofin Turai

Kofin Turai

A jiya aka fara fafata wasannin cin kofin nahiyar turai  gasar da yakamata ace an buga a shekara ta 2020 amma sakamakon bullar annobar cutar Korona yasa dole aka dage zuwa wannan shekarar.

Tawagar ‘yan wasan kasar Italy ce ta fara buga wasan da tawagar kasar Turkiyya a wani wasa mai zafi kuma wasan shi ne wasan farko da aka fara a gasar ta bana a babban filin wasa na Olympic dake birnin Rome.

A wasan yau da za’a fafata tawagar ‘yan wasan kasar Wales ce zata fafata data Switzerland sai kuma wasa na biyu tsakanin Denmark da Finland sai kuma wasa na uku a yau Asabar din tsakanin Belgium da Russia.

Tuni tawagogin kasashe na kwallon kafa da dama dai tuni suka bayyana sunayen ‘yan wasan da za su wakilce su a gasar wadda zata samu halartar manya manyan ‘yan wasa da  matasa a duniya.

Exit mobile version