Huzaifa Dokaji" />

Jiya Da Yau: Alakar Kasuwanci Tsakanin Nijeriya Da Daular Saudiyya

Alaka tsakanin Nijeriya da daular Saudiyya alaka ce mai tsawo da dimbin tarihi. Addinin Musulman Nijeriya dai, wanda suka mamaye Arewaci da wani bangare na Kudancin kasarnan, addini ne daya samo asali daga Daular Saudiyya. Kusan ma a iya cewa, babu wani mutum da yake da daraja a idon Musulman Nijeriya a duk fadin duniya irin Balarabe. Dalilan hakan sun hada da cewa yaren Larabci yaren Annabi ne (SAS) kuma Larabawa yan’uwan Annabi (SAS) ne. Har ta kai a gun Bahaushe, misali, ba daraja irin ace a cikin nasabar ka kana da alaka da Larabawa, ko kana da ilimi a harshensu.
Tarihin zamantakewa tsakanin wandannan al’ummai biyu ya fara ne daga zuwan Shehu Muhammad al-Maghili kasar Kano. Shehu al-Maghili kamar yadda wani aji na masana suka rawaito, ya zo ne daga Madina, sakamakon mafarki da yayi da Annabi (SAS) da ya ce masa ya taho yamma ya yada addinin Musulunci. Shehu al-Maghili ya debo kasar garin Madina ya taho da ita yana gwadawa da kasar duk garin daya sauka. Ba ta yi daidai da kasar ko ina ba, sai ta Kano, in da hakan ya nuna masa cewa nan ne Annabi (SAS) ke nufinsa da zuwa! Shehu Maghili ya zo Kanon a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499), in da har ya rubuta wa masa littafin “Taj al-Muluk”, wanda ya zama kundin tsarin mulkin ta na farko. Zuri’ar sa sune, har yau, suke rike da sarautar Sarkin Sharifai, a fadar Kano.
Tun daga nan, kofa ta budewa Larabawa, musamman na Afirka ta Yamma, in da Kano ta zama cibiyar su ta tallan haja, addini, akida da ala’ada, musamman daga farkon karni na sha biyar, in da kasar Hausa ta fara cin moriyar kasuwancin Sahara. Litattafan addini na mazhabar Malikiyya, wadda mazhaba ce ta Madina, su ka fara bulbulowa kasar Kano. Ilimi ya kara yaduwa, Kano ta kara tabbatar da matsayin ta a cikin garuruwan Musulunci! Ta kai mutanen Kano na ganin a duk duniya bamda Madina ba inda ya kai su son Manzan Allah (SAS)
Mutanen Arewacin kasarnan da wani sashe na Yarabawa sun fara zuwa kasar Saudiyya tun tsahon lokaci. Tun suna zuwa a kafa da taimakon dabbobi, har zuwa karni na 20 da Bature ya kawo musu mota da jirgin sama. Tafiyar, a da, tana daukan kamar shekaru biyar, a matsakaicin lissafi. Wasu matafiyan na rasuwa a hanya, wasu kuma sukan yada zango a Sudan, ko Misra, wasu kuma igiyar ruwa ta kada su Yemen. Bisa kiyasi, idan mutum ashirin suka tafi, wadanda ke dawowa ba sa fin biyu ko uku. Zuwan Jirgin saman Turawa ya saukaka hakan, in da dubban mahajjata ke tafiya, kuma baifi ace goma sun rasu ba. Sarkin Kano Abdullahi Bayero, shine Sarkin Kano na farko da a shekarar 1934 ya fara zuwa kasar Saudiyya don sauke farali a jirgin sama.
Yan Nijeriya sun taka rawar gani a tarihin Daular Saudiyya, kama daga kafa daular da Ahalin Abdallah Saud su ka yi har ya zuwa yau. A shekarar 1925 da rikici ya balla tsakanin magoya bayan Sa’ud dana Sharif Hussain, wanda yake gwamnan daular Ottoman, yan Nijeriya goyon bayan su ya rabu biyu, wa su sun goyawa Sharif Hussaini baya, wasu kuma sun goyawa Ahl Saud. Koma dai ya abin yake, bayan kafa daular, Hausawa sun sami martaba a idon duka bangaroron biyu. Martabar Hausawa a idon sabuwar Daular Saudiyya, ta kai shaidar Hausawa ba a haufi a kanta a tsakanin mahukuntan kasar ta Saudiyya. Ko yan doka ne suka zo sasanta wata takaddama, matukar da dan Nijeriya, to fa duk shaidar da ya bayarta zauna!
Tsahon lokaci mafi yawan sana’ar yan Nijeriya a kasar Saudiyya bata wuce dinki, siyar da gwajo, girki, siyar da abinci, gadi, sana’ar chanji, awon kaya a filin jirgi, tukin mota, aikin kamfani, Leburanci da sauran dai yan kananan sana’o’i. Ko da yake akwai tsirarun yan Nijeriya a Saudiyya da suke da karatun zamani, dokokin Saudiyyan kan zamar musu matsala wajen samu aiki. Rashin takardar zama ta ighama, ita ce babbar cikas da yan kasarnan le fuskanta wajen gabatar da al’amuran su. Shin me yasa samum ita ighamar yake da wuya? Bayan tsaurara matakan samu takardar da mahukuntan kasar su kai, akwai kuma lalacewar yan Nijeriyar suma!
Wani abun takaici shine, a lokacin mulkin Sarki Faisal, ya yi yunkurin tantance yan kasa da baki, kuma aka sanar cewa dukkan mai son zama dan Kasa yaje ya karbi takardar, kyauta. Abin dariya za a ace ko al-ajabi, wani Takari da yake bani labari, yan Nijeriya har Allah ya isa suka dinga yiwa yayan su idan suka karbi takardar. Fafur, tamkar jarumin da yake kai naushi dan gudun mutuwa, suka rufe ido suka ki karbar izinin zama yan kasar. Kamar yadda jikokin wadanda hakan ta faru da su suka sanar dani a wani bincike a dandalinsu dake Hajj Camp, hatta wani mutum da ya dinga goya jakar takardun a bayan sa ana zaga unguwanni da shi a Makkah, ana bin gida-gida ana tallatawa mutane takardar tumda a lokacin mutane ake nema su zauna a raya kasar, har ya mutu ba shi da ita! Da kyar da jibin goshi jikan sa, bayan shekaru, ya samu!
Wata kila hakan na da nasaba da talaucin da kasar ta Saudiyya take ciki a wancan lokacin, wanda hakan ya sa Yan Nijeriya jin cewa kasar su tafi arziki, saboda haka ibada kadai ke kai su Saudiyya, ba zama ba. Yau gashi yan Nijeriya na neman takardar da kudin su, ana wulakanta su. Uhm! Duniya juyu juyi, wai kwado ya fada ruwan zafi! Ba abin mamaki bane idan akai la’akari da cewa duk wamda ya san kasar Saudiyya kafin ta fara morar arzikin man fetir din ta da ga 1950s, kasashe irin Nijeriya sun fi ta wadata da arziki. Ta kai a lokacin da Masallacin Juma’a na sarki na Kano ke da wutar lantarki, bangarori da dama na Masallacin Harami mai tsarki, fitulun gargajiya ake kunnawa!
Rashin wannan takarda yasa yanzu Yan Nijeriya suna cikin mafi yawan masu zaman da ake kira zaman shahada, wato zaman ba bisa ka’ida ba. Hausawan da ke da mutunci kwarai a idon mahukuntan Saudiyya, wanda a da can yarda ta sa suke aiki a gidan kudi, a dora musu buhunan kudi su kai ma’aikata su kadai, yanzu kudin su ma abin tuhuma ne, balle wani ya basu na shi amana. Dama dai wanda ya ki sharar Masallaci, ai dole zai yi ta kasuwa. Rashin tanadin dan Nijeriya da yawa yake!
Duk da wannan tsohuwar alaka, abin takaici ne ace babu wata yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin wadannan kasashe biyu. Babu wata doka da take bawa dan Nijeriya kariya akan kasuwancin sa a Daular ta Saudiyya, haka zalika wadda za ta karfafawa yan Saudiyyan kwarin gwiwar kafa kamfanoni a Nijeriya. Kasashen da Nijeriya ta kulla wannan yarjejeniya da su kamar Kasar Sin da Amurka, alakarsu bata kai tsufan ta Saudiyya da Nijeriya ba. Wannan yasa wadanda suke son gudanar da halastaccen kasuwanci da zai kunshi kudade masu dimbim yawa ke fuskantar barazanar rashin kariyar diplomaciyya ga dukiyoyin su. Hakan na da hadari kwarai da gaske, duba da yanda yanzu yan Nijeriya ke fuskantar rushewar martaba a hannun mahukunta da mutanen Daular ta Saudiyya saboda yawan marasa gaskiya da suke mamaye harkar.
Akwai bukatar gwamnati ta maida hankalinta kwarai wajen yin wannan yarjejeniya, domin da yadda kasar Saudiyya ke bajakolin akidar ta ta addini, a Arewacin Nijeriya an dan sirka da cinikayyar kasa da kasa da kwarai tabbas talakawan Arewa sun fi amfana. Yarjejeniyar kuma zata saukaka harkar Kano-Jidda wadda ke addabar mahukutan Saudiyya, da safarar mutane da ake, wanda hakan ke kara zubarwa da mutanen Nijeriya mutunci a idon duniya. Karyewar harkar ta Kano-Jidda ta sa yawan dukiyar da ke gudama tsakanin al’ummar kasarnan da ta Saudiyya ya ragu kwarai.
Lallai ya kamata gwamanti ta dubi barazanar da karyewar Naira ke yi ga yan kasuwar Nijeriya da suke gudanar da kasuwanci a kasar ta Saudiyya da idon rahama domin babu dalilin kyale wannan kasuwanci mai dimbin tarihi ya rushe. Akwai matsala babba, idan aka ce akida kadai mutanen Arewa ke amfana da Daular Saudiyya, domin idan aka duba batun da kyau, za a ga kusan babu in da Nijeriya ta ke morar Saudiyya, in banda ta fuskar ilimi, ilimin ma na siyasar akida. Alakar kuwa ta wuce a barta iya haka, musamman a wannan zamani da kasuwanci ne ginshikin alaku. Alakar addini alaka ce mai girma kuma abar so, tilas kuma a yabawa kasar ta Saudiyya wajen ilmantar da matasan kasarnan da take yi. Sai dai kuma dole ne a dubinwasu fuskokin ma alakar kasa da kasa, dan haka rubutun ke kiran mahukunta su kara duba wasu bangarorin da kasashen biyu zasu kara amfanar juna.

Exit mobile version