JKS Za Ta Gabatar Da Takaitaccen Tarihin Harkokinta Na Shekaru 100

Daga CRI Hausa,

Za a bude cikakken zama shekara-shekara na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin a ranar 8 ga wannan wata a birnin Beijing, wanda ya yi matukar janyo hankalin ciki da wajen kasar.

A matsayin jam’iyya mai mulki mafi girma a duniya dake jagorantar mutane fiye da biliyan daya da miliyan 400, jam’iyyar kwaminis ta Sin ta bi tunanin kiyaye zaman lafiya na duniya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, da kuma raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama yayin da take daidaita harkokin kasa da kasa.

Jakadan kasar Angola dake kasar Sin João Salvador dos Santos Neto yana ganin cewa, “A ganina tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gabatar zai sa kaimi ga jama’ar dukkan duniya da su hada kai don tinkarar kalubale tare.

Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gano wannan hanya da samar mana wannan sabuwar hanya don gaya mana cewa za a warware matsaloli ta hanyar hadin kan kasa da kasa.

Mu jam’iyyun kasashen Afirka muna bukatar irin wannan sabon tunani, kana JKS ta samar mana karin goyon baya. Ina imani da cewa, za mu iya kirkiro kyakkyawar makoma tare, da hada kan jama’ar kasa da kasa don tinkarar kalubale na yanzu da na nan gaba tare.” (Zainab Zhang)

Exit mobile version