Daga Yusuf Shu’aibu,
A ranar Laraba ce, Kungiyar Musulmi ta JNI suka mayar da martani ga shugaban Cocin Katolika na Jihar Sakkwato, Mathew Hassan Kukah bisa kalamansa na ranar Kirsimeti. Inda ta zarge shi da jifar addinin Musulunci da kibiya mai matukar dafi a cikin sakon nasa.
A cikin kalaman Jama’atu Nasril (JNI) ta siffanta kalaman Kuhah a matsayin kibiya wanda ya soki addinin Musulunci da shi, da ka iya janyo tashin hankali da kuma rarrabuwar kai a tsakanin mabiya addinin Musulunci da kuma Kiristoci.
A cikin takaidar da JNI ta fitar wanda Sakatarenta, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya rattaba hannu, ta ce, Kukah yana daya daga cikin mambobin kwamitin zaman lafiya amma a kullum kalamunsa yana kawo hargitsi da ya shafi addini da kabilanci wanda zai iya haifar da rarrabuwar kai a tsakanin Arewaci da kuma Kudanci.
JNI dai ta yi zargin cewa a maimakon Kukah ya isar da sakon fatan zaman lafiya da hadin kai da kuma tausayi musamman ma a cikin wannan yanayi da kasar take ciki; sai ga shi ya buge da kawo abin da zai haddasa husuma.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kukah yana zaune ne a Jihar Sakkwato wacce ita ce Babbar Daular Musulunci da ke fadin yankin Afirka. Duk da jiha ce ta Musulmai tun a tarihi, amma an yi maraba da zuwan Bishop Kukah, inda aka amshe shi hannu bibbiyu, sannan aka ba shi masauki ba tare da nuna masa wani bambamcin addini ba.
“Bai kamata Bishop Kukah ya soki addinin Musulunci ba. Domin addinin Musulunci, addini ne na zaman lafiya wanda ya hana tashin hankali da kuma martaba Dan’adam ko da ba musulmi ba.
“Domin haka, Manzan Allah (SAW) ya gargadi Musulmai a kan kar su jawo tashin hankali da su zauna lafiya, wannan yana daga cikin Hadisi.
“Kukah yana zaune ne a yankin Arewacin Nijeriya kuma yana abokantaka da sauran Musulmai. Yana gudanar da mu’amularsa ba tare da jin wata tsoro ba da Musulman da ke Arewacin Nijeriya. Sun ba shi wajen zama da dukkan goyan bayan da yake bukata.
“Bishop Kukah yana jin dadinsa da walwala a Jihar Sakkwato kamar yadda kowani Musulmin da yake Arewa yake ji, amma a sakonsa na Kirsimeti ya jefi Musulunci da Musulmai da kibiya mai matukar dafi.
“Kafin wannan, ya dade yana sukar addinin Musulunci da musulmai, amma a wannan karo, ya rasa dankantankar da yake da shi da al’ummar Musulmai. Ta yaya Musulmai za su yarda da mutumin da yake faran-faran da fuska da rana, amma kuma da dare yana cin zarafin addinin Musulunci? Ta ya ya Musulmai za su ci gaba da mu’amula da irin wannan mutumin? Ta ya ya Musulmai za su yarda da mai yi wa addininsu zagon kasa?
JNI ta bukaci daukacin Musulmai da su ci gaba da zaman lafiya tare da bin doka da kuma kin amincewa da rikici a wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu. Ya kamata Musulmai su hada kai kamar yadda addinin Musulunci ya karantar. Mu ci gaba da dangantarmu da sauran makotanmu Kiristoci duk da irin sabanin da aka samu,” in ji JNI.