Bello Hamza" />

John McCain Ya Rasu

Iyalan Sanatan Amurka John McCain sun ce ya rasu dazun nan, kwana guda bayan sun sanar cewa ya daina yin jinyar cutar kansar kwakwalwa, a cewar kafar labaran Fod News ta nan Amurka, McCain ya rasu ya na da shekaru 81 a duniya.
Jiya Jumma’a su ka bayar da sanarwar cewa ya daina shan magani, inda su ka ce, MacCain “ya ma yi tsawon rai” tun bayan da ya bayyana ma jama’a bara cewa ya na da wannan cutar.
Marigayi McCain ya yi ta jinyar wannan mugunyar cuta ta kansar kwakwalwa tun daga watan Yulin 2017.
Duk da yinkurin da ya yi har sau biyu na neman zama Shugaban Amurka, wato a 2000 da kuma 2008 ba tare da nasara ba, McCain ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yan Majalisar Dattawan Amurka. McCain, wanda dan Republican ne, ya kan hada kai da ‘yan Democrat da ma ‘yan jam’iyyarsa ta Republican, kan abuwan da su ka hada da dumamar yanayi da sauye-sauyen tsarin shigi da fici, da kuma batun ka’idar kudin kamfe.

Exit mobile version