Connect with us

WASANNI

Juventus Ce Za Ta Sake Lashe Siriya A, Cewar Totti  

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Roma kuma darakta a kungiyar, Francisco Totti, ya bayyana cewa kungiyar Jubentus ce zata sake lashe gasar siriya A ta wannan kakar sannan kungiyoyi irinsu Roma zasuyi kokawar neman zama na biyu zuwa na hudu.

Kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dai ta lashe gasar siriya A sau bakwai a jere sannan kuma wannan shekarar ma ta dauki hanya bayan ta kashe makudan kudade wajen siyan dan wasa Cristiano Ronaldo daga Real Madrid.

Sai dai har yanzu Ronaldo bai zura kwallo a raga ba a wasannin da kungiyar ta buga amma kuma duk da haka Juventus din itace a mataki na daya tun yanzu bayan ta lashe wasanninta uku cikin wasanni uku da aka fafata a gasar.

“Kungiyar Juventus tazama zakara da kanta. Babu kungiyar da zata iya taka mata burki a gaba daya kungiyoyin da suke buga gasar siriya A a yanzu” in Totti

Yaci gaba da cewa “Roma ta dade rabonta data lashe siriya A kuma har yanzu babu niyyar sake lashewa amma ragowar kungiyoyi ko tunanin hakan basayi saboda karfin Juventus yanzu gaba daya mun zama ‘yan rakiya”

Ya kara da cewa abinda Roma yakamata tayi kawai shine ta dage taga ta kammala gasar a matsayi na biyu ko kuma na hudu su samu tikitin gasar zakarun turai su cigaba da buga wasa kawai a haka.

Rabon da wata kungiya ta lashe kofin Siriya  A ba Juventus ba tun shekara ta 2011 da kungiyar kwallon kafa ta AC Millan ta lashe kuma a shekarar Juventus s matsayi na bakwai ta kammala kakar wasan.

 
Advertisement

labarai