Juncao, Ciyawar Da Ke Rungumar Makomar Dan Adam Ta Bai Daya
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Juncao, Ciyawar Da Ke Rungumar Makomar Dan Adam Ta Bai Daya

byCMG Hausa
3 years ago
Juncao

Jama’a, ko kun taba jin sunan Juncao? Wannan wata nauin ciyawa ce da ake iya amfani da ita wurin noman laimar kwado da ake iya mai da ita abinci ko magani, wadda ake kiranta ciyawar kasar Sin ko ciyawar samar da arziki a kasashe da dama.

A shekarun 1980, noman laimar kwado ya zama muhimmin aiki da manoma ke dogara a kai wajen saukaka fatara a lardin Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Sai dai hakan ya haifar da matsala a sakamakon yadda manoma suke yawan saran bishiyoyi don yin amfani da su wajen noman laimar kwado.

  • Ya Kamata Amurka Ta Koyi Darasi Daga Yakin Harajin Da Bai Yi Nasara Ba Kan Sin

Ganin haka ya sa Mr. Lin Zhanxi, kwararren masanin ilmin noma da dazuzzuka na kasar Sin, da abokan aikinsa, suka yi kokarin nazari tare da gano fasahar noman laimar kwado ta amfani da nau’in ciyayin Juncao a maimakon katako, a wani kokari na daidaita matsalar.

Ta hakan, yawan dazuzzukan da ake sara domin noman laimar kwado ya ragu da yawan gaske. Baya ga haka, sakamakon yadda ciyayin Juncao suka kasance masu iya jure yanayi mai wahala, wadanda kuma suke da saiwoyi masu karfi, baya ga kuma yadda suka kasance masu gina jiki, ya sa bayan noman laimar kwado, ana kuma amfani da su wajen magance iska, da kwararowar hamada, da kuma kiwon dabbobi, wato ke nan, ciyayin na iya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da kuma kiyaye muhalli duka.

Daga nan, sai Lin Zhanxi ya yayata fasahar zuwa gundumomi 506 na fadin kasar Sin, fasahar da ta taimaka wajen bude kofar samun arziki ga al’umma da ke fama da talauci a kasar.

A bara, akwai wani wasan kwaikwayon talabijin da ya yi matukar samun farin jini a kasar Sin, wanda ya bayyana yadda malami Lin Zhanxi ya yayata fasahar Juncao daga Fujian har zuwa yankin Xihaigu na jihar Ningxia, da ke arewa maso yammacin kasar Sin, ta yadda manoman yankin suka saukaka fatara ta hanyar noman laimar kwado.

Malami Lin Zhanxi bai tsaya a gida ba, a maimakon haka, ya kara yayata fasahar zuwa sauran kasashe da shiyyoyin duniya 106.

A Lesotho, ya kafa tsarin noma da ke iya samar da laimar kwado da nauyinsu ya kai ton 1.2 a kan fadin kasa da bai wuce muraba’in mita 10 kacal ba, matakin da ya zama muhimmiyar kafar samun karin kudi shiga ga manoman wurin.

A kasar Rwanda, kwamitin kula da ayyukan gona na kasar ya yayata fasahar Juncao a sassan kasar wajen kare matsalar lalacewar gonakin kasar. Lallai, ciyayin Juncao sun zama ciyayin samar da arziki da alheri ga al’ummar kasashe masu tasowa da dama.

Daga ranar 16 zuwa 22 ga wata, an gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis dake kan karagar mulkin kasar Sin karo na 20 a birnin Beijing, kuma Malami Lin Zhanxi ma ya halarci taron a matsayin daya daga cikin wakilai 2296 na jam’iyyar.

A yayin da yake halartar taron, ya kuma kiyaye tuntuba da abokan aikinsa. Wani lokaci, ya kan kuma tashi da tsakan dare, don yin musayar ra’ayoyi tare da takwarorinsa na kasashen Afirka da Latin Amurka.

Rahoton da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron na wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, ya yi nuni da cewa, “Kullum kasar Sin na nacewa ga bin manufar diplomasiyya, ta kiyaye zaman lafiyar duniya da tabbatar da samun ci gaban juna, don rungumar makomar dan Adam ta bai daya.” “kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa da kasashe masu tasowa bisa sahihanci da gaskiya, don kiyaye moriyarsu ta bai daya”.

A game da wannan, malami Lin Zhanxi ya bayyana cewa, “Kasar Sin na samar da gudummawar fasahohinta a fannin ayyukan gona ba tare da gindaya wani sharadi ba, kuma muna samar da sahihiyar gudummawarmu, don fatan ganin an saukaka fatara.”

A shekarar 2020, kasar Sin ta cimma nasarar fitar da al’umma kusan miliyan 100 a karkarar kasar Sin daga kangin talauci, kuma kasancewarta kasa mai tasowa mafi girma a duniya, ba ta manta da sauran kasashe masu tasowa ba, har ma ta raba musu fasahohinta ba tare da boye komai ba, don rungumar makomar dan Adam ta bai daya. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Bayelsa: Peter Obi Ya Ziyarci Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bayelsa 

Bayelsa: Peter Obi Ya Ziyarci Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bayelsa 

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version